✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da ya sa na kirkiro shirin ‘Taurarin Zamani’ – Ofime

Dan Najeriya mazaunin kasar Kanada, kuma mai shirya fina-finai, Rogers Ofime ya bayyana cewa kamfaninsa mai suna Natibe Media ya kirkiron shirin talabijin mai suna…

Dan Najeriya mazaunin kasar Kanada, kuma mai shirya fina-finai, Rogers Ofime ya bayyana cewa kamfaninsa mai suna Natibe Media ya kirkiron shirin talabijin mai suna ‘Taurarin Zamani’ ne don ya nuna arewacin Najeriya ga duniya.

Rogers Ofime wanda kuma darakta, wanda ya shirya manyan fina-finan Turanci na Nollywood irinsu ‘Price of Spice’ da kuma ‘Olaibiri’ ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da Aminiya a garin Jos.

Daraktan ya ce, shirin Taurarin Zamani zai nuna manya masu fada a ji da ke Arewacin Najeriya.

Ya ce, “Mun samu damar tattaunawa da manyan masu fada a ji ’yan Arewa, wadanda suka yi fice a bangarori da dama da suka hada da siyasa da aikin gwamnati da kasuwanci da kuma fitattu a bangaren waka da kida da kuma masana’antar fina-finan hausa ta Kannywood.”

Ya kara da cewa a bangaren nishadi sun tattauna da Ali Nuhu da Rahama Sadau da mawaki Umar M Shareef da jarumi Sadik Daba da Yakubu Muhammad da Sani Danja da mawaki Ahmad Mai Shanawa da Classik da sauransu.

Fitaccen Furodusa kuma jarumin fina-finan Hausa, Usman Uzee ne yake gabatar da shirin, inda ya kuma tattauana da fitattun mutane irinsu Jerry Gana da Sarah Jibril da Zainab Bagudu da Halima Idris da kuma Hon. Munirat Suleiman.

Sauran wadanda suka bakunci shirin sun hada da Husseini Coomasie da Sanata Nenadi Usman da Hon. Aminu Goro da Isaac Dabid Balami da sauransu.

Ya bayyana cewa tuni aka fara nuna shirin ‘Taurarin Zamani a tashar Hausa ta Africa Magic a ranar Asabar da misalin 5:30 na yamma da kuma maimaici a ranar Lahadi da misalin 5:30 na yamma. 

Ofime wanda ya shirya fina-finan da ake nunawa a talabijin da suka hada da ‘Tinsel’ da ‘The Johnson’ ya ce an kuma fara nuna shirin a gidan Talabijin na Liberty.