✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da ya sa na hada kayan kida da waka a dakina – Mawaki Umar

Za mu fara da gabatar da kanka Assalamu alaikum, sunana Umar M. Lawan, an haife ni a garin Kano, sannan ina zama a garin Abuja,…

Za mu fara da gabatar da kanka

Assalamu alaikum, sunana Umar M. Lawan, an haife ni a garin Kano, sannan ina zama a garin Abuja, na yi makarantar firamare a  Model Primary School da ke Maitama, sannan karamar makarantar sakandare a Model Junior Secondary School da ke Maitama a Abuja, daga bisani  na kammala karatun sakandare a Gobernment Day Senior Secondary School da ke Abuja, inda a yanzu nake neman gurbin karatun Digiri a daya daga cikin jami’o’in kasar nan. 

Me ya ja hankalinka har ka shiga harkar waka? 

Gaskiya abin da ya ja ra’ayina na fara waka ba komai ba ne illa ina matukar son in ga na kasance daya daga cikin wadanda za a rika alfahari da su a bangaren yada al’adun Bahaushe da kuma taimakawa wajen isar da sako cikin hanya mafi saurin zuwa ga al’umma.

Ka kai kimanin shekara nawa kana waka?

Gaskiya na kai kimanin shekara hudu ina waka, kuma akalla wakokina za su kai 150.

Wacce wakarka ka fi so a cikin wakokin da ka yi? Kuma me ya sa?

Gaskiya na fi son wakar ‘MAI LAIFI’ saboda waka ce wacce wadanda suka dauka ina shirme a baya, wato ma’ana ba su dauki abin da nake yi da muhimmanci ba, inda a yanzu sun gamsu da cewa tabbas ba shirme nake yi ba, domin wakar har yau ban ji an kushe ta ba.

Wane mawaki kake koyi da shi a harkar waka?

Eh, to, gaskiya akwai mawakin da nake koyi da shi wanda a kan wakokinsa na san yadda waka take, wannan mawaki kuwa ba kowa ba ne face Nura M Inuwa, kuma abubuwan da na koya daga gare shi su ne, akwai abin da ake kira kafiya a cikin yaren waka, wanda a Turance ana kiransa rhymes, ma’ana idan ka fara dora waka da harafin (b), to ka zama ka sauke da harafin (b) din, sannan  idan son samu ne da abin da ka sauke amshi da shi, ya zama da shi za ka kare kowane baiti.

Wane kalubale ka fuskanta a harkar waka?

Eh to, a zahirin gaskiya tabbas na fahimci kalubale daga gidanmu, amma kalubalen ba wai a kan in daina waka ba, sai don a cewarsu na fifita zuwa studio a kan kula da kaina, musamman wajen cin abinci, domin akwai lokutan da nake kai har karfe dayan dare ban dawo gida ba, hakan ya bata ran ’yan gidanmu sosai, har ta kai ga an yi mini fada an gaji, har aka bude mini studio a cikin dakina domin in daina takura kaina, daga nan kuma shi ke nan.

Wane buri kake so ka cimma a harkar waka?

Umar Lawan: Babban burina a harkar waka shi ne in kasance mai tsaftace harshena a cikin kowace kalmar da zan furta a cikin wakata, ma’ana ya zama ko za a kushe ni, to ya kasance ba a cikin kalmar bakina ba, wannan shi nake fata.

A wadansu lokuta ana yi wa mawaka kallon mutane banza, ko me za ka ce a kan hakan?

Eh to, gaskiya idan na ce mawaka mutanen banza ne na zalince su, sannan idan na ce duka mawaka mutanen kirki ne na yi son kai, saboda babu inda za a gina ya kasance kowa nagari ne, ko kuma kowa na banza ne, babu inda babu nagari da bata-gari, iyakar abin da zan iya kara tunatar da mutane ke nan, sannan don Allah a rika tabbatar da duk abin da ake zargi kafin yanke hukunci.

Yaya batun fara wakar fina-finai kuma?

Eh, to, muna nan muna sa rai a kodayaushe, amma mafi akasarin masu shirya fina-finai ba su yarda da cewa su sa wakar mawaki a fim ba, duk dadinta sai dai idan ya zama wani, amma ba dukansu ba ne haka, domin akwai masu kokarin tallafa wa matasan mawaka ta hanyar ba su wakokin manyan fina-fina ba tare da duba matsayinsu ba, matukar za su yi da kyau.

Me ya sa ka fi mayar da hankali kan wakokin soyayya? 

Eh to dalilin da ya sa nake yin wakar soyayya a cikin mafi akasarin wakokina shi ne, ita soyayya ita ce ba ta da iyaka, tana da farko amma karshenta ya wuce tunanin mai tunani, ka ga kuwa ke nan idan har akwai abin da karshensa ya wuce tunani, to shi ya kamata a kasance da shi musamman ta hanyar da ta shafi nishadantarwa.

Wane lokaci ka fi jin dadin yin waka?

Duk lokacin da mutane suka kira ni suka yaba wakata, kuma suka kara mini kwarin gwiwa, suka yi mini addu’a, to a lokacin ne zafafan wakoki suke kara shiga kwalkwalwata.

Ka dauki tsawon shekara hudu kana waka, zuwa yanzu wadanne nasarorin ka cimma?

daya daga cikin manyan nasarorina shi ne, samun dimbin masoya wadanda su ne komai a duniya, sannan wakokina sun yi sanadiyyar nishadantar da mutane, inda wadansu suka fadakar da su. Haka abin alfahari ne a gare ni, kuma babbar nasara ce a wuria.