✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da ya sa na dawo harkar fim gadan-gadan – Iyantama

Hamisu Lamido Iyantama fitaccen jarumi ne kuma Furodusa, inda kuma yake shugabantar kamfanin shirya fim na Iyantama Multimedia, kamfanin da ya yi fice wajen shirya…

Hamisu Lamido Iyantama fitaccen jarumi ne kuma Furodusa, inda kuma yake shugabantar kamfanin shirya fim na Iyantama Multimedia, kamfanin da ya yi fice wajen shirya fina-finai masu inganci. A shekarun baya an daina jin duriyarsa har wadansu suke ganin ya daina harkar fim ne, dalilin haka ya sanya Aminiya ta tattauna da shi, inda ya bayyana dalilin da ya sa aka daina jin duriyarsa na dan wani lokaci, inda a yanzu ya bayyana dalilinsa na dawowa cikin harkar fim gadan-gadan. Ga yadda hirar ta kasance:

 

Masu kallo sun daina ganinka a fina-finai, sannan ba a ganin fina-finan da ka shirya, ko me ya jawo haka?

Ba ja da baya na yi wajen shirya fim ba, mutane su sani shi fim shirya shi na bukatar natsuwa da tunani, yana bukatar ka zo da abin da idan ka yi shi, mutane za su so shi, za su kuma karbe shi. Ko a lokutan baya ba na sakin fim da yawa, nakan yi daya, biyu a shekara,  haka ta taho tunda na fara harkar fim. 

Yanzu da harkar ta zamo wata iri, kasuwanci ne ya lalace, wato tun daga bidiyo kaset aka fara aka zo faifan CD, har abubuwa suka jagwalgwale, mutum ya zuba kudi ya yi fim dinsa daga karshe ya nemi kudin ya dawo sai ya ga bai dawo ba, ka ga sana’ar fim sana’a ce ta zuba kudi ka nemi riba duk da cewa akwai manufa ta yada al’adu da sanya abubuwan da suka shafi addini, duk da haka idan ka zuba kudi ka ga bai dawo ba, to za ka ji tsoron gudun asara, wannan shi ne dalilin da ya sa aka dan ja baya. 

Wannan ne ya sa muka natsu, muka yi tunani sannan muka ga wace hanya za a zo da ita don a ci gaba da wannan sana’a ba tare da tsoron faduwa ba. 

 

A yanzu me ya sa hankalinka ya dawo harkar fim?

A yanzu akwai wasu hanyoyi da suka kunshi gidajen talabijin, kuma kasuwannin silima sun dawo, da ma can ana yi ba yanzu aka fara ba, tunda aka fara Kannywood ana kai fim silima, inda a nan ma kake mayar da kudi, kafin ya fito kasuwa. Yanzu ka ga akwai silimomi a Shoprite da kuma wasu da ake so a kara fadadawa, hakan ya sa na dawo harkar fim.

 

Yanzu bayan ka dawo harkar fim, ka yi fina-finai kamar nawa?

A bara na yi fina-finai kamar bakwai, a cikin fina-finan akwai ‘Uwar Bari’ da ‘Wayar Hannu’  fina-finai ne a kan harkar iyali, sai ‘Wuta A Makera’ a kan masana’antar fim, sai ‘dan Baiwa’ fim ne a kan mawaki kuma mai shirya fim, sai fim din ‘Hakki’, wato na karshe ke nan. Amma har yanzu babu wanda ya fito a cikinsu.

 Duk wadannan fina-finai akwai sakonni masu kwari, ina kuma yi wa mutane albishir cewa idan fina-finan bakwai suka fito hakika za su gane cewa ba wai fim ne ba a iya ba, an iya daidai gwargwado.

Wanda ya ba da umarnin wadannan fina-finai bakwai mutum daya ne, wato Hafizu Bello, fitaccen darakta ne a Kannywood, kuma masu kallo sun san ya yi fina-finai masu inganci.

 

A shekarun baya ka yi ayyukan fina-finai, ga kuma yanzu da zamani ya canja a harkar, a ganinka me ya bambanta aiki a wancan lokacin da kuma yanzu?

A baya an yi fina-finai, sannan a wannan karnin ma an yi fina-finai, a yanzu kullum duniya canjawa take yi, canjin shi ne yadda abubuwa suke canjawa a kai-a-kai, kyamarorin da muke amfani da su a baya a da din da muke amfani da su su ne masu kyau, kuma babu sama da su, amma duk shekara daya biyu sai ka ga an sake fitowa da sabuwar fasaha, bambancin da da kuma yanzu shi ne kayan aiki, na baya analogue ne, na yanzu kuma digital ne. 

Sannan a bangaren fitilu na da dole idan babu wutar lantarki ba za ka yi fim ba, amma yanzu an yi fitilun zamani masu batiri, inda za ka iya awa 12 kana daukar fim. 

 

Ka yi aiki da tsofaffin jarumai a wancan lokacin, yanzu akwai sababbin jarumai, a ganinka wani abu ne babba ya bambanta jaruman yanzu da na da?

Duk dai babu wadanda babu a cikin fina-finan nan bakwai da na yi, akwai tsofaffin jarumai kamarsu Baballe Hayatu. Shi fim yana bukatar ka duba shi don ganin cewa kana bukatar sabuwar fuska ce, ko a’a, akwai fim din da idan za ka yi idan har ka dauko sabo to zai wahalar da kai, ko ya bata maka lokaci, saboda bai goge ba, hakan ne zai sa ka dauki tsofaffin jarumai ka sanya.

Akwai fim din da idan za ka yi to sabon jarumi labarin yake bukata. Akwai wurin da ma ni na ga ya cancanta in fito, sai in biya kaina in fito a ciki. Sababbin jaruman da na yi amfani da su sun hada da Halima Ibrahim da Garzali Miko da Fatima AbdurRahman da Wasila Abubakar da sauransu.

 

Ka dade kana harkar fim, kuma a wancan lokacin akwai matsalolin da kuka fuskanta, yanzu bayan ka dawo harkar gadan-gadan wadanne matsaloli kake fuskanta?

A zahirin gaskiya tunda na fara wadannan fina-finai ban fuskanci wata matsala da za a ce ta a-zo-a-gani ba, kodayake na fuskanci matsala daya zuwa biyu, na samu matsala daga wurin masu daukar sauti, kamar yadda aka kawo su suka yi aikin na yi zaton kwararru ne, amma sun ba ni matsala, sai da na zo tacewa da hada hotuna sai na ji sautin bai dauku da kyau ba, saboda haka bayan na biya su sai da na sake kira jaruman suka zo studio muka dauki muryarsu muka sake dorawa. Sun janyo mana asara. 

Matsala ta biyu ita ce mafi yawancin masu tace hotunan fina-finai suna da rashin hakuri, idan kuka yi yarjejeniya da mutum kuka fara aiki, sai ka ga cikin lokacin kankane har ya gaji, ni ina yi aikin tace hotuna ne kamar yadda na koya a wajen masana, su kuma ba haka suka iya ba, ba su aikin ake yi, darakta ya tafi ya bar su, su yi yadda suke so, mu kuwa ba haka muka koya ba. Kuma mai hada hotuna zai sanya mana abin da muke so ne, ba wai ra’ayinsa ba. 

 

Wane buri kake so ka cimma?

Ba ni da wani buri da ya wuce burin mutanen da suka san fina-finai irin nawa, da kuma masu burin ganin kamfanina ya dawo ya ci gaba da yi musu fina-finai, domin a kullum ka shiga cikin jama’a, gaban manya da sarakuna da malamai za su ce kun daina fim, kun bari yara sun lalata sana’ar fim, don Allah ku dawo. 

Buri na farko shi ne mu dawo mu yi irin abin da mutane suke da bukata, kuma ko da ba a samu riba mai yawa ba, in dai mutane za su samu abin da suke bukata, to shi ke nan, kuma daga nan idan mutane suka gano an dawo sayen fina-finai irin namu, an fara gudun marasa inganci, domin mafi yawan fina-finan da ake yi shirme ne, kamar yadda jama’a suke fada, amma akwai fina-finai nagari masu kwatanta abin da ya kamata.

Wani lokaci za mu ga sun yi kokari, ina da burin sauya akalar fim daga inda take a yanzu.

Buri na biyu shi ne mu daga kasuwar fim daga inda take a yanzu, wato mu fara kai fina-finai kasashen waje, irin su Kamaru da Chadi da Nijar da sauransu, muna so a je can silimominsu a rika haska fina-finanmu, shi ya sa ma fina-finaina bayan an yi musu fassara ta Ingilshi, za a yi da Larabci da Faransanci, domin burinmu shi ne mu fadada kasuwancin fim.

Sannan ina da burin yin hadaka da wadansu masu harkar fim da ke kasashen ketare, don mu hada jari da su domin mu kara samun kasuwar kasashen waje – a Nahiyar Turai da ta Larabawa da sauransu.

 

Daga karshe wani sako kake da shi ga masu karatu?

Ina so su jira fina-finan kamfanina bakwai din nan da za su fito, ina so masu kallo su yi hakuri da mu, idan mun yi fina-finan da ba su gane ba, to akwai lambar waya a jikin kwalin fina-finanmu, sai su kira mu yi musu bayani. Sannan a wannan shekarar da muke ciki ta 2018 ina yi wa masu kallo albishir din cewa ina shirin yin fina-finai 10.