✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da ya sa na bai wa Sarki Sanusi II mukamai – El-Rufai

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufai, ya bayyana dalilansa na bai wa tsohon sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II mukamai biyu a jihar Kaduna. Ya…

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufai, ya bayyana dalilansa na bai wa tsohon sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II mukamai biyu a jihar Kaduna.

Ya ce, ya ba tsohon sarkin Kano mukaman ne saboda abokinsa ne tun suna kuruciya, kuma ya kasance yana taimakonsa dan haka shima yake kokarin ya saka wa sarkin da dan abin da zai iya yi.

El-Rufa’i, ya ce tsohon sarkin Kano mutum ne mai tarin ilimi da ke da martaba a fadin duniya kuma ya ba shi mukamin na domin jihar Kaduna ta amfana ta kuma samu ci gaba da tarin iliminsa.

A daren yau ake saran gwaman Nasiru El-Rufa’i zai yi wa tsohon sarkin Kano rakiya zuwa jihar Legas daga birnin Abuja inda gwamna jihar Legas Babajide Sanwo-Olu zai tare su.