Manyan gobe tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. Ya karatu, ina fata kuna karatu sosai don ku ci jarrabawa musamman a wannan lokaci da ake neman fara yin jarrabawa don a ba ku hutu.
Taku, Lubabatu I. Garba
A yau na kawo muku wani labari mai dadi ne da na yi wa taken: “Dalilin da ya sa kafafuwan gizo-gizo suka zama sirara. Na san Manyan gobe za ku ji dadin wannan labari, don haka sau ku bi labarin a hankali don ku fahimci darasin da ke cikinsa.
A zamanin da an yi wani gizo-gizo mai tsananin kwadayi. Duk da cewa matarsa ta iya abinci sosai, hakan bai hana shi kwadayin abincin makwabta ba. Wata rana gizo yana yawonsa sai ya biya ta gidan abokinsa Zomo. Yana shiga sai ya ji kanshin abinci na tasowa daga tukunya sai ya ce wa zomo “Kai! wannan kanshin fa, me kake girkawa ne?”. Sai Zomo ya gaya masa cewa yana dafa shinkafa da miyar ganye ne. Ya ce masa “Yanzu haka ma ya kusa dahuwa idan kana son ci ka tsaya.”
Sanin cewa idan ya tsaya jiran abincin zomo zai nemi ya taya shi wani aiki sai gizo-gizo ya ce “Gaskiya zan so in ci, sai dai yanzu sauri nake akwai wurin da za ni. Abin da za a yi shi ne zan saka yana wacce zan daura bangare daya a jikin kafata daya kuma a jikin tukunyarka.
Idan abincin ya yi sai ka ja yanar, idan na ji haka sai na yi sauri na zo.”
Da gizo-gizo ya tafi sai ya zo wucewa ta gidan biri sai ya ji kanshin wake sai ya tsaya suka gaisa da biri. Sai biri ya ce masa “Ga shi ka zo abinci bai gama nuna ba”. Sai gizo-gizo ya ce masa “Kada ka damu zan je in dawo, amma kafin na tafi bari na saka wata ’yar yana wacce zan daure guda a kafata daya kuma a jikin tukunyarka. Da zarar waken ya nuna sai ka ja yanar ni kuma sai na zo na ci.”
Za mu cigaba a mako mai zuwa insha Allah