✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da ya sa Jaruma Priyanka ta zama a bar koyi a gare ni – Rahama Sadau

Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa, Rahama Sadau ta bayyana cewa dalilan da ya sa shahararriyar jarumar fina-finan Indiya Priyanka Chopra ta zama mata  a bar koyi…

Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa, Rahama Sadau ta bayyana cewa dalilan da ya sa shahararriyar jarumar fina-finan Indiya Priyanka Chopra ta zama mata  a bar koyi gare ta su ne yadda jarumar Indiyar take jajircewa da kuma nuna hazaka a duk lokacin da take aikin fitowa a fina-finanta. 

Rahama Sadau ta kuma kara da cewa tana samun kwarin gwiwa a wurin Priyanka don fuskantar rayuwa da kuma kalubalen da ke cikin masana’antar fina-finai.

Jarumar ta bayyana hakan ne a shafinta na Twitter a lokacin da take bikin cikar shekarar jaruma Priyanka 16 a sinimar masana’antar fina-finan Indiya da aka fi sani da Bollywood.

“Na fara ganin jaruma Priyanka Chopra a Kismat a shekarar 2004, a lokacin da na ganta sai na ga kamar ina kallon kaina ne, hazakarta, jajircewarta da kuma fikira da basirarta sun ja hankalina. Na kasance daga cikin mutanen da suke koyi da ita, wadda ta kuma zame musu wani sikeli a rayuwa,” inji Rahama.