✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da ya sa Filato United ta sallami ’yan wasa 11 – Albert

Bayan cece-kucen da batun korar ’yan wasa 11 da kulob din Filato United ya yi a ranar Asabar din da ta gabata, kulob din ya…

Bayan cece-kucen da batun korar ’yan wasa 11 da kulob din Filato United ya yi a ranar Asabar din da ta gabata, kulob din ya bayyana cewa rashin da’a da kwazo da kuma hakuri ne na wadansu ’yan wasa ya sanya kulob din ya sallame su.

Mai magana da yawun kulob din, Albert Dakup a lokacin da yake tattaunawa da Aminiya a garin Jos, ya bayyana cewa ba da wata mummunar manufa kulob din ya yi sallamar ba, sai don su samu damar yin kyakkyawan shirin tunkarar gasar badi.

Korar dai ta shafi ’yan wasan gaba da suka hada da Ogbonna Annayor da John Kim da kuma Longi Obadiah, inda ’yan wasan baya kuma suka hada da Okoro Obasi da kuma Olowo Emmanuel.

’Yan wasan tsakiya sun hada da Chima Ndukwu da Daddy Morris da Daddy Francis da Umar Umara da kuma Stanley Okoro. Korar ta kuma shafi gola Ayo Segun.

Albert Dakup ya kuma kara da cewa za a kara ba dan wasa Musa Adamu da kuma Myep Bulus-Ghai dama don su nuna bajintarsu a gasar badi, sakamakon a bara wadannan ’yan wasa sun yi fama da rashin lafiya, sannan sun ji rauni.

“Mun dauki hukuncin sallamar ’yan wasan ne don mu yi kyakkyawan shirin fuskantar Gasar Zakarun Afirka da Gasar Firimiya da kuma da ta Aiteo Cup badi, yanzu da muka sallami wadannan ’yan wasan za mu cefano wadanda suke da sanin makamar buga kwallo, don mu samu ’yan wasan da za su kara daukaka martabar kulob dinmu.” Inji shi.

Ya ce zuwa yanzu kulob din yana tattaunawa da ’yan wasa shida, kuma nan ba da jimawa ba za su bayyana cefanansu ga duniya.