Rikicin da ake yi a Arewacin kasar Habasha ya sa mutane miliyan biyu sun rasa muhallinsu, wadansu sama na tsananin bukatar agajin abinci.
Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Antony Blinken ya yi bulaguro zuwa Kenya, inda ya tattauna kan rikicin makwabciyarta Habasha.
- Hatsarin jirgin ruwa ya yi ajalin ’yan mata bakwai a Jigawa
- Na yi alkawari zan yi nazari kan sakin Nnamdi Kanu — Buhari
Tuni aka umarci mutanen Amurka da Birtaniya su fice daga kasar tun ana da sauran jiragen fasinja kamar yadda Ministan Birtaniya ya bayyana. W
annan shawara da aka bayar da kuma waiwaye kan abin da ya faru a Kabul a watan Agusta, an bayar da ita ce a daidai lokacin da alamu suka nuna cewa dakarun ’yan tawaye daga Arewacin Tigray ka iya dannawa babban birnin kasar, Addis Ababa.
Shekara guda da fara Yakin Basasar, wanda ya jefa jama’a cikin mummunan yanayi, a bangare guda kuma kasashen duniya na jan hankalin bangarorin biyu kan abin da rikicin zai haifar ga kasar.
Matsin lambar da kasashen Afirka da jami’an diflomasiyyar Amurka ke yi wa Habasha na karuwa, kuma hakan babban tasiri zai yi ga yankin da duniya baki daya.
Me ya sa aka damu?
Adadin wadanda lamarin ya shafa daga bangarorin biyu zai yi matukar tasiri ga yankin da duniya baki daya.
Akalla mutanen yankin dubu 400, ne suke cikin barazanar rashin abinci, yayin da yankin ke fama da rashin magungunan da ake bukata, sai kuma wadansu sama da miliyan biyu da aka tilasta wa tserewa daga gidajensu.
Ana zargin gwamnati da hana kayan agaji shiga yankin Tigray da gangan, zargin da ta musanta.
Haka kuma, akwai shaidun da suka nuna cewa an yi ta kashe mutane, da azabtar da su, da cin zarafi ta hanyar lalata da dukkan bangarorin biyu suka aikata. Amma akwai wata manufa da suke da ita kan rikicin.
Kasar Habasha mai yawan al’umma miliyan 110, ita ce ta biyu mafi yawan jama’a a Nahiyar Afirka, ta kasance mai kwanciyar hankali kuma babbar kawar kasashen Yammacin Duniya.
Ana fargabar matukar tashin hankalin ya ci gaba, wannan ka iya janyo darewarta gida biyu sakamakon yawan kabilun da ake da su.
Idan miliyoyin mutane suka tsere daga yankunan da ake tashin hankalin, to zai yi matukar wuya makwabtansu su samu kwanciyar hankali.
Kasar Habasha ta yi iyaka da kasashe shida, biyu daga ciki na fama da tashin hankali wato Sudan ta Kudu da Somaliya, yayin da sauran irin Sudan ba a dade da yin juyin mulki ba.
Dakarun Habasha na cikin kawancen dakarun Tarayyar Afirka da na Majalisar Dinkin Duniya da ke yaki da mayakan Al-Shabab a Somaliya, ana kuma fargabar za su iya janyewa idan kasashensu suka bukaci haka.
Su ma dakarun Eritireya sun dade suna mara wa gwamnatin Habasha baya, kuma su ma lamarin na iya shafarsu.
A farkon wannan wata, dubban mutanen kasar ne suka cika titunan birnin Addis Ababa domin nuna goyon baya ga gwamnati a yakin da take yi da ’yan tawayen TPLF A watan da ya gabata, Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya ruwaito cewa kasar Turkiyya ta amince ta sayar wa kasar Habasha jirage marasa matuka.
Wannan yarjejeniya na barazana ga kyakkyawar dangantakar da take tsakanin Turkiyya da kasar Masar, wadda dama suke da jikakkiya a tsakaninta da Habasha kan batun mallakar Kogin Nilu.
Har wa yau, Habasha ta sayo makamai daga kasashen China da Iran, sannan an yi amfani da jiragen Hadaddiyar Daular Larabawa wajen kai makaman, kamar yadda rahoton shafin Intanet na Oryd ya ruwaito.
Amurka, ta dade tana kallon Habasha a matsayin babbar aminiyarta, musamman lokacin yaki da ta’addanci.
Habasha ta taimaka wajen yaki da masu tayar da kayar baya a Somaliya, sojojin Habasha su ne a sahun gaba ta wannan fannin, ta kuma yi wa Amurka tayin amfani da sararin samaniyarta a lokacin yakin Iraki.
Tana daga cikin tsirarun kasashen Afirka da suka shiga kawance da Amurka.
Kwanciyar hankali da zaman lafiya a kasar Habasha na da matukar muhimmanci ga kawayenta, musamman Amurka wadda ke taimakawa da kudade, ta kuma kai agajin sama da Dala biliyan hudu a tsakanin shekarar 2016 zuwa 2020.
Sai dai wakilin Amurka na musamman a yankin, Jeffrey Feltman, ya zargi gwamnatin Habasha bisa matakan da take dauka a yaki da ’yan tawayen Tigray, wanda ya janyo mummunar yunwa a kasar.
A kan me ake yin yakin?
Ya samo asali ne kan rashin daidaituwa a tsakanin Firayi Minista Abiy da Kungiyar TPLF, wadda kusan shekara 27 suka mamaye madafun ikon kasar Habasha tare da mai da yankin Tigray saniyar ware.
A shekarar 2018 ne Mista Abiy ya zama Firayi Ministan Habasha, bayan zanga-zangar da kabilar Oromo suka yi.
Da ma Oromo sun dade suna jan ragamar mulkin kasar, inda shi kansa Mista Abiy dan kabilar Oromo ne, kuma yana daga cikin kawancen da ke jan ragamar kasar da kuma ake yi wa kallon wanda zai kawo karshen rikicin da ke shimfide a kasar.
A kokarin kawo sauyi, wanda yake amfani da siyasa da wanzar da zaman lafiya da dadaddiyar alaka da makwabciyar kasar Eritiriya, sai yankin Tigray ya ga an ware shi gefe guda.
Shekara daya ta da gabata ne rashin jituwa ya fito fili a tsakanin Mista Abiy da ’yan tawayen kungiyar ’yantar da yankin Tigray (TPFL), inda yaki ya barke a tsakaninsu.
An dai zargi ’yan tawayen Tigray da kai hari kan sansanin sojin gwamnati tare da sace makamai, don haka gwamnatin Habasha ta mayar da martani, lamarin da ya kara kazancewa tare da janyo tashin hankalin da har yanzu ya ki ci, ya ki cinyewa.