dan kwallon gaba a kulob din Manchester United dabier Hernandez da aka fi sani da Chicharito ya bayyana dalilin da ya sa ya gwammace ya zabi Cristiano Ronaldo na kulob din Real Madrid da ke Sifen fiye da dan kwallon FC Barcelona da ke Sifen Lionel Messi a fagen kwallo.
Chicharito wanda ya koma kulob din Madrid ana gaba da rufe kakar saye da sayar da ’yan kwallo a matsayin aro na shekara guda kimanin kwanaki 10 da suka wuce ya ce isarsa kulob din Madrid ke da wuya ya fahimci lallai Ronaldo ya fi Messi a fagen kwallo nesa ba kusa ba.
Ya ce ganin yadda dan kwallon yake fito da sababbin dabaru a kullum ta sa ya fahimci lallai Ronaldo ya shiga gaban Messi.
Chicharito, dan kimanin shekara 26 ya yi wadannan kalamai ne a lokacin da yake hira da jaridar El Chiringuito da ke Sifen a ranar Talatar da ta wuce a lokacin da suke atisaye.
Dalilin da ya sa Cristiano Ronaldo ya fi Lionel Messi -Chicharito
dan kwallon gaba a kulob din Manchester United dabier Hernandez da aka fi sani da Chicharito ya bayyana dalilin da ya sa ya gwammace ya…