Shugaban Rasha, Vladmir Putin, ba zai samu damar halartar jana’izar Sarauniyar Ingila ba, Elizabeth II da ta riga mu gidan gaskiya a ranar Alhamis.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da dankartaka ke kara tsami tsakanin Putin da kasashen Yamma dangane da mamayar da yake yi a Ukraine.
- An dakatar da wasannin Firimiya saboda mutuwar Sarauniyar Ingila
- Fadar Buckingham ta fara zaman makokin Sarauniya Elizabeth II
Haka kuma zumuncin da ke tsakanin Rasha da Birtaniya ya ja bayan da ba a taba ganin makamancinsa ba tun bayan Yakin Cacar Baka wato Cold War.
Sai dai a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Fadar Kremlin, Dmitry Peskov ya fitar, ya ce ya zuwa yanzu ba a yanke shawarar wanda zai wakilci Putin yayin jana’izar ba wadda za a gudanar ranar 19 ga watan Satumba a Westminster Abbey.
Dmitry Peskov ya bayyana cewa duk da yadda Sarauniyar ke da matukar muhimmanci da kima ga shugaba Putin, amma yanayi ba zai ba shi damar halartar jana’izar ba.
Tun a jawabin alhini da ya fitar a ranar Alhamis jim kadan bayan mutuwar Sarauniya Elizabeth, shugaba Putin ya bayyanata a matsayin jajirtacciya da ta samar da ci gaba mai dorewa.
Kazalika, al’ummar Rasha a hukumance ta gudanar jimamin mutuwar sarauniyar mai shekaru 96 wadda ta shafe shekaru 70 a kan karaga.