✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da saura kiris Najeriya ta shawo kan matsalar tsaro — Buni

Gwamnatin Buhari ma ta yi kokari wajen bai wa jami’an tsaro ingantattun kayan aiki.

Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya ce a zabar sabbin shugabannin tsaro da Shugaba Bola Tinubu ya yi cikin tsanaki, ya sa saura kiris Najeriya ta kawo karshen kalubalen tsaro da take fuskanta na tsawon shekaru. 

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka wa Gwamna Buni kan harkokin yada labarai, Alhaji Mamman Mohammed ya raba wa manema labarai a Damaturu.

A cewar sanarwar, mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, zai yi amfani da kwarewarsa wajen yaki da matsalar tsaron da ke addabar sassa da dama na kasar nan.

“Haka zalika sabbin hafsoshin tsaron na da kwarewa matukar, lamarin da ’yan Najeriya ke da kwarin gwiwar kan wadanda aka mika wa akalar jagorancin yaki da rashin tsaro a kasar nan.

“A matsayinmu na mutanen jihohin da ke sahun gaba ta fuskantar matsalar tsaro, muna yaba wa Gwamnatin Tarayya da hukumomin tsaro bisa gagarumin nasarorin da aka samu a jihohin namu da ma wasu bangarorin kasa.

“Muna da kwarin gwiwar cewa a matsayin su  na masu himma wadanda suka taka muhimmiyar rawa wajen samar da zaman lafiya a jihohin, sabbin shugabannin muna da yakinin za su kara kara kaini wajen kawo karshen kalubalen rashin tsaro gaba daya a kasar da Yardar Allah SWT.

“A lokuta daban-daban sun nuna jarumta da kwarewa a ayyukan da suka shafi tsaro  na kasa.

“Don haka a hakikanin gaskiya zan iya cewa, Shugaban Kasa ya yi zabi mai kyau kuma za mu ci gaba da bayar da goyon baya ga duk ayyukan tsaro a yankinmu,” inji shi.

Ya kara da cewa, “Malam Nuhu Ribadu kwararren jami’in tsaro ne wanda zai yi aiki tare da jami’an tsaro domin cimma manufar da aka sa gaba.”

Gwamnan ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su mara wa sabuwar gwamnati da sabbin hafsoshin tsaron baya domin samun nasara a kan wannan lamari.

Ya yaba wa gwamnatin tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kan yadda ta samar da ingantattun kayan aiki na harkokin tsaro wadda hakan ya taimaka wajen kara karfafa gwiwar jami’an tsaron a ko’ina cikin kasar nan domin ganin aikin da aka ba su an samu nasara a kansa.

“Wannan gagarumin kokarin sun kara wa jami’an tsaro kwarin gwiwa wajen yaki da matsalar tsaro yadda ya kamata, kuma tare da nuna jajircewa,” inji Gwamna Buni.