✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dalilin da na ki fita jinya ketare —Osinbajo

Kwararrun likitoci shida ne suka yi wa Osinbajo tiyata a wani asibiti a Legas.

Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya bayyana dalilinsa na kin fita kasar waje domin yin jinyar gurdewar da ya yi a kafa yayin motsa jiki.

Aminiya ta ruwaito cewa, a karshen makon ne nan aka kwantar da Mataimakin Shugaban Kasar saboda wani rauni da ya samu a kafarsa yayin buga wasan Squash, lamarin da ya kai ga an yi masa tiyata.

A wata hirarsa da Muryar Amurka, hadimin Mataimakin Shugaban Kasar kan Harkokin Siyasa, Abdulrahman Bappah Yola, ya bayyana cewa, Osinbajo ya zabi likitocin Najeriya su duba shi don gwada misali da amincewa da kwarewar su.

A cewar Abdulrahaman Bappah, kwararrun likitoci shida ne suka yi wa ubangidansa tiyata a wani asibiti da ke Birkin Ikko da aka kammala cikin nasara.

Likitocin da suka yi wa Osinbajo tiyata

Ya ce kwararrun likitoci 6 da suka hada na kashi da masu kashe radadin ciwo ne suka yi wa Mataimakin Shugaban Kasar aiki a asibitin Duchess da ke Ikeja a Legas.