Tsohon Shugaban Kasar Afghanistan, Ashraf Ghani, ya ce ba shi da zabi face ya cika wandonsa da iska ya bar kasar lokacin da mayakan Taliban suka tunkaro babban birnin kasar na Kabul a watan Agusta.
A cikin wata tattaunawarsa da BBC wacce aka yada ranar Alhamis, tsohon Shugaban ya ce ’yan mintuna kawai aka bashi a lokacin kan ya yanke shawarar barin kasar.
- Buhari ya gana da Jonathan a Aso Rock
- Masu kudin Najeriya na da hannu dumu-dumu a matsalar tsaro – Al-Mustapha
Sai dai bayanan nasa sun ci karo da na tsohon Shugaban Kasar, Hamid Karzai, da na gwamnatin Amurka.
Ashraf Ghani ya kuma musanta zarge-zargen da ake masa cewa ya gudu ya bar kasar ne da miliyoyin kudaden da ya sace.
Guduwar tsohon Shugaban dai ranar 15 ga watan Agustan ta dada jefa Kabul cikin rudani, a daidai lokacin da dakarun Amurka da na NATO ke kammala shirye-shiryen ficewa daga kasar bayan shafe shekara 20 suna gwabza yaki da Taliban.
“Ranar da abin zai faru da safe, ko tantama ban yi ba kan cewa dole na gudu kafin rana,” inji Ashraf Ghani.
To sai dai Hamid Karzai ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AP a farkon wannan watan cewa matakin na Ghani, ya wargaza damar da masu shiga tsakani, ciki har da shi da kuma Shugaban kwamitin, Abdullah Abdullah suke da ita ta cimma yarjejeniya da mayakan na Taliban.
Karzai ya kara da cewa gabanin guduwar ta Ashraf Ghani, mayakan na Taliban har sun amince su dakata a iya wajen birnin na Kabul.
To sai dai ya ce lokacin da ya kira Ministan Tsaro na lokacin da takwaransa na Cikin Gida da shugaban ’Yan Sanda amma ya gano cewa dukkansu sun gudu daga kasar, sai ya gayyato Taliban domin su shigo su kare birnin da mutanen cikinsa daga fadawa rudanin masu sace-sace.
Amma Ashraf Ghani ya shaida wa BBC cewa ya gudu ne domin gujewa tarwatsa Kabul, inda ya ce bangarorin Taliban guda biyu da ba sa ga-maciji da juna na shirin gwabza yaki tsakaninsu kan wanda zai karbe iko da birnin a lokacin.
Tun bayan karbar mulkin na Taliban dai, dubban ’yan kasar ne suka gudu suka nemi mafaka a wasu kasashen saboda fargabar fuskantar musgunawa daga sabuwar gwamnatin.