✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da mutane ke tunanin ina abu irin na ’yan kwaya

– Kwamishinan ’Yan sandan Kano Alhaji Mohammed Wakili shi ne sabon Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kano wanda ake yi wa lakabi da: “Maza kwaya, mata…

– Kwamishinan ’Yan sandan Kano

Alhaji Mohammed Wakili shi ne sabon Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kano wanda ake yi wa lakabi da: “Maza kwaya, mata kwaya,” bayan da wani bidiyo da ke yawo a shafin sada zumunta ya nuna shi yana bayyana haka. Sabon Kwamishinan ya yi fice kan yakin da yake yi da shan kwaya da hakar daba, inda a cikin kwana goma ya kama daruruwan ’yan daba da masu tu’ammali da kwaya da kayan maye. A tattaunawar da ya yi da Aminiya ya yi tsokaci game da aikinsa da kuma sabon sunan da ya samu da sauran batutuwa.

Aminiya: Tun daga lokacin da ka hau wannan kujera ta Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kano sai ka fara da yaki da shan kwaya da harkar daba, me ya sa kake da ra’ayi a wannan bangare?

Wakili: Ina ganin irin tasirin abin da wadannan abubuwa suke haifarwa ya sa na zabi wannan  bangare na kuma dauki abin a matsayin aiki mai muhimmanci. Na fahimci irin abin da hakan yake haifarwa ga al’umma a karshen lamari. Wannan ya sa na yi tunanin zan iya yin wani abu a kai komai kankantarsa don magance matsalar. Ba zan iya nade hannuna in bar abubuwa

irin wadannan su ci gaba da faruwa ba, ba tare da na bayar da tawa gudunmawar wajen hana faruwarsu ba.

 

Aminiya: Rahotanni sun bayyana cewa ka samu nasara a lokacin da ka yi irin wannan yakin a Jihar Katsina. Wace irin nasara ka samu a can?

Wakili: Ina tunanin kamata ya yi mutanen Katsina su yi min hukunci a kan haka. Abu mafi muhimmanci shi ne na san dai na yi duk aikin da na yi ba saboda in samu wani abu a wurin kowa ba, sai dai ina yi ne don aiki ga  al’ummata da kasata gaba daya. Dukan abin da nake yi ina yi ne saboda Allah saboda kuma al’ummata.

 

Aminiya: Akwai wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sad zumunta inda kake magana a kan shan kwaya wanda har ka samu lakabin “maza kwaya, mata kwaya” kasan da wannan kuwa?

Wakili: Eh, ina sane da hakan sai dai kwata-kwata bai dame ni ba, to me ya sa abin zai dame ni?

Kowa yana fadin ra’ayinsa game da yadda yake kallon lamurra. Na ma ji wadansu suna fadin cewa kamar ni ma ina shan kwayarwato a buge nake wanda kuma ba haka ba ne. Ina da burin bayar da ’yar tawa gudunmawar ce don rage harkar shaye-shaye a jihar nan. Saboda na fahimci irin yadda shaye-shaye ke wargaza rayuwar al’umma.

 

Aminiya: A ganinka me ya sa mutane suke tunanin kana shaye-shaye?

Wakili: Watakila saboda yanayina ne hakan da kuma yadda nake gudanar da abubuwana. Ina tunanin haka ne ya sa suke tunanin ina shaye-shaye. Gaskiya haka yanayina yake ina yin abu  ina rangaji da juyawa da sauran  motsa jikina wanda mutane suke daukarsa a abin dariya kuma abin da ba su saba gani ba. A gaskiya  haka yanayina yake. Haka Allah Ya halicce ni. Kuma ba zan iya yin komai a kan hakan ba. Ban taba shan kwaya ba. Kai ban taba ganin kwaya ba har sai da na fara aiki dan sanda. Kai ban ma taba jin sunayen wasu daga cikin nau’o’in kwayar ba.

 

Aminiya: Mu koma batun yaki da kake yi da shan miyagun  kwayoyi da kuma harkar daba a ina ka tsaya?

Wakili: A gaskiya yanzu aka fara sai dai zuwa yanzu mun kama  dubban ’yan daba da wadansu  daga cikin masu kawo kwaya.

Muna fata za mu kai ga kama sauran dillalan kwayar, saboda  su ne babbar matsalarmu. Mun  gurfanar da yawa daga cikin ’yan

dabar da muka kama a gaban kotu wadanda kuma na aike da  su kurkuku a matsyain masu jiran shari’a yayin da ake ci gaba da bincike. Muna fata wadanda muka gurfanar za a yanke musu  hukunci saboda girman laifin da  suka aikata. Muna kula da cewa

kafin mu kama mutum sai mun tabbatar muna da hujja a kansa.

 

Aminiya: Wane kira kake da shi ga sauran abokan aiki kamar Hukumar NDLEA da NAFDAC  da Kwastam da Hukumar Shigeda-

Fice da sauransu?

Wakili: Kamata ya yi a hada hannu don magance lamarin,  Allah Ya yi wa kasar nan albarka.  Muna da shugabanni nigari  masu hangen nesa wadanda kuma suke son talaka. Akwai  dokoki da aka ajiye wadanda ya  kamata mu bi don ciyar da kasar nan gaba. Hukumomi da aka ambata an ba su wuka da nama  wajen sauke nauyin da aka dora  musu ta hanyar bin dokokin da aka shimfida wanda hakan zai ciyar da kasar gaba. Abin da ke  gabanmu kawai a matsayinmu na jami’an tsaro shi ne mu yi aikin da aka dora mana. Idan dukan hukumomin tsaro suka amince za  su yaki harkar kwaya to wallahi za mu yi aiki mai kyau.

 

Aminiya: Wane kira kake da shi ga malamai da sarakuna? 

Wakili: Wadanan su ne  manyan masu ruwa-da-tsaki saboda mabiyansu suna girmama su. A duk lokacin da suka yi nagana, abiyansu

suna saurar, don haka suna da muhimmanci wajen wannan yaki  da kwaya da kuma daba.  Sarkin Kano ya damu sosai game da wannan abu, yana kuma iyakar kokarinsa wajen ganin  an magance wannan lamari. A  kwanan nan na ji yana kira don a kara karfafa aikin da ake yi na yaki da miyagun kwayoyi.