Gwamnatin Jihar Oyo ta sanar da cewa ba da wata manufa ga Musulmin Jihar ta sanya ranar tantance sabbin malaman da ta dauka aiki ranar Sallah ba.
Shugaban hukumar makarantun gaba da firamare na jihar TESCOM, Fasto Akinade Alamu ne ya bayyana hakan yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai a Ibadan, inda ya ce har yanzu ana kan tantance sabbin malaman, wanda hakan ke nuna ba don wata manakisa aka sanya har da ranar Sallar ba.
- Yadda Najeriya ta ciyo bashin tiriliyan N225 a shekara 20
- ’Yan bindiga sun kashe, sun sace ’yan yawon Sallah a Katsina
Kazalika ya ce ya yi mamaki da Kungiyar Al’ummar Musulmi ta MURIC ta nuna kin amincewarta da wannan hukunci na gwamnatin, saboda Gwamnatin Tarayyya ta sanya ranar Litinin da Talata a matsayin ranakun hutu a kasa baki daya domin ba wa Musulmi damar bukukuwan Babbar Sallah.
Sai dai Faston ya ce hanzarin gwamnatin kan wannan batun shi ne tun kafin Gwamnatin Tarayya ta ba da waccan sanarwar, ta jihar ta ayyana makon baki daya a matsayin wanda za ta gudanar da tantancewar, da nufin kara inganta gaskiya da amana a tsarin daukar ma’aikatan da gwamnatin jihar ta yi.
Ya ce: “Yana da matukar muhimmanci a fahimci cewa aikin tantancewar da ake yi ba yana nufin hana al’ummar Musulmi cin gajiyar hutun Sallah da Gwamnatin Tarayya ta bayar ba ne, sai don tabbatar da bin doka da oda wajen daukar ma’aikata a sassa, da ma su kansu hukumomin gwamnatin.
“Aikin dori ne kan wanda aka fara a makon da ya gabata, kuma muna so ne mu tattara bayanan ma’aikatan gwamnatin jiha da aka dauka tun shekara biyu baya zuwa yaznu, domin mika su ga kundin adana bayanan ma’aikatar kudi”, in ji shi.
“Da farko mun tsara fara aikin a karshen mako, amma sai muka dakatar a ranakun Asabar da Lahadi saboda Musulmin su samu damar yin bikin Babbar Sallah.
“Saboda haka, abin mamaki ne wata kungiya ta fito ta ce shirin da aka dauko da nufin tabbatar da gaskiya, an bullo da shi ne don a cusguna wa Musulmi ne bayan Gwamnatin Tarayya kanta ta ba su hutu.
“Irin wadannan zarge-zarge kuskure ne babba da rashin fahimta, hadi da yarfe ga kyakkyawar bayyananniyar aniyar gwamnatin jihar.”, in ji shugaban hukumar.