Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya kare matsayarsa ta zabar tsohon gwamnan Jihar Borno, Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa na Zaben 2023, yana mai cewa ba zai yiwu ya zabi Musulmi da Kirista a lokaci guda ba.
Gabanin bayyana Shettima a matsayin abokin takara, an dai yi ta cece-kuce a kan tsayar da abokan takara da suke kan akidar addini daya ba.
A yayin da kungiyar Mabiya Addinin Kirista ta Najeriya (CAN) ta ce ba za ta sabu ba tare da gargadi a kan yin hakan, wasu masu ruwa da tsaki sun hakikance a kan cewa a mayar da hankali zuwa ga cancanta ba tare da la’akari da addini, kabila ko yankin da abokanan takarar suka fito ba.
Abin da ya sa na zabi Kashim Shettima
Da yake zayyana dalilinsa na zabar Shettima, Tinubu ya ce a duk rayuwarsa, babu wata shawara da zai yanke ko wani hukunci da zai zartar game da mabiyansa face ya yi la’akari da kaidodin cancanta, tausayi, mutunci, riko da gaskiya da amana da kuma nagarta.
Da yake magana game da sulhu da Shettima, Tinubu ya ce duk rayuwarsa, yanke shawara game da tawagar da ke kewaye da shi da kuma goyon bayansa a koyaushe suna bin ka’idodin cancanta, kirkire-kirkire, tausayi, mutunci, gaskiya, da kuma riko da nagarta.
Ya ce ya yi tuntube-tuntube kan batun zabar abokin takararsa, kuma ya yaba da ta ra’ayoyin jiga-jigan jam’iyyar da abokan siyasa wadanda a cewarsa sun kasance tamkar shi da babu abin da suke hange face makomar Najeriya.
Tinubu ya ce jagoranci nagari, kwarewa da kuma duba ya zuwa wanda zai tafiyar da kowa wajen riko da madafan iko, su ne ginshikan da ya yi la’akari da su wajen zabo abokin takararsa.
“Ina da cikakkiyar masaniya game da akidar addinin abokin takarata wanda kuma mutane adalci da daraja sun ankarar da ni a kan haka.
An bani shawarwari
“An samu wadanda suka bani shawarar cewa na zabo abokin takarar daga addinin Kirista domin na faranta wa Kiristoci, wasu kuma sun shawarce ni a kan zabar Musulmi domin faranta wa Musulmai, sai dai a bayyane take cewa ba zai yiwu na dauki duk shawarwarin biyu a lokaci guda ba.
“Duk bangarorin biyu sun gabatar da kwararan hujjoji da dalilai bisa ga madogara ta abin da suke ganin zai kawo ci gaban kasar nan..
“..sai dai na lura cewa babu ko daya daga cikin shawararin da ta yi daidai da abin da nake hange wanda kuma ba shi ne hakikanin abin da Najeriya take bukata ba a yanzu.
“Idan aka ce yau ni ne Shugaban Kasa, zan yi fatan ganin na yi jagoranci da zai kai kasar nan zuwa tudun mun tsira ta hanyar daukar wasu matakai da ba kasafai aka saba yi ba, da kuma yanke wasu shawarwari wadanda akwai yiwuwar su bambanta da tsari na siyasa.
“Saboda haka a irin wannan lokaci, dole a yi watsi da wannan tsare-tsare na siyasa sannan a kafa tubalin shugabanci na gaskiya da hakikanin jagoranci wanda ya tsarkaka da adalci.
Ina alfahari da zabin da na yi
“A yau [Lahadi] ina mai alfahari da wannan zabi da na yi na abokin takara saboda na yi shi ne ba tare da laakari da addini ba kuma don na faranta wa wani yanki ko wata alumma ko wani abu makamancin haka ba.
“Na yanke wannan hukunci ne saboda ina da yakinin cewa wannan mutumi [Kashim Shettima] zai taimaka min wajen yi wa duk ’yan Najeriya jagoranci mai nagarta ba tare da nuna wariya ga kowace kabila, yanki ko addini ba.
‘Kar hukuncin da na yanke ya bakanta wa wasu rai’
Ga wadanda wannan mataki ba zai yi musu dadi ba, Tinubu ya ce, “ina mai sanar da ku cewa, musamman wadanda za su ji takaicin zabin da na yi saboda ra’ayin da suka rika na addini, ina so su sani cewa ba zan taba watsi da sha’anin bambancin addini ko na kabilu da muke da su a kasar nan ba.
“Yin la’akari da hakan wani muhimmin bangare ne da zai bude kofar jagoranci nagari, sai dai kuma dole mu kwana da sanin cewa addini, kabilanci ko yanki ba su da wani tasiri kan makomar tafarkinmu a matsayin kasa.
“Don ganin an samu ci gaba a kasar nan da hadin kai, sai mun rabu da duk wani daurin gindi da mu da shi na akidar addini ko kabila ko yanki, mun sake daidaita lissafin siyasarmu zuwa ga cancanta da kuma adalci.