✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba za mu fitar da Aminu Bayero daga Fadar Nassarawa ba — ’Yan sanda

Jami’an tsaro sun yi wa Fadar Nassarawa ƙawanya sun hana shige da ficen ababen hawa.

Kwamishinan ’yan sandan Kano ya ce ba za su bi umarnin Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya buƙaci su fitar da Sarki Aminu Ado Bayero daga Fadar Nassarawa ba.

Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar wa BBC ta wayar tarho.

Kwamishina Usaini Gumel ya ce aiwatar da umarnin gwamnan tamkar wuce gona da iri ne, la’akari da cewa har yanzu taƙaddamar tana gaban kuliya.

Usaini ya ce gwamnatin Kano da ta bayar da umarnin, ita ce kuma ta shigar da ƙara a wata babbar kotun jihar kan umarnin fitar da Aminu Ado, shari’ar da za a fara zama a kai ranar Litinin, 24 ga watan Yuni.

“Idan muka bi umarnin, zai kasance kamar muna yin aikin kotu ne saboda ba mu san me zai faru a kotun ba,” in ji Gumel.

Bayanai sun ce an dai tsaurara matakan tsaro a fadar ta Nassarawa inda Sarki Aminu Ado Bayero yake zaune.

A jiya Alhamis ce Kwamishinan Shari’a na Kano, Barista Haruna Isa Dederi ya bayar da umarnin fitar da Sarkin Kano na 15 daga gidan sarki na Nassarawa, inda ya ce za a soma rusau da yi wa katangar gidan kwaskwarima.

Wannan dai na zuwa ne bayan hukuncin da wata Babbar Kotun Tarayya da ke jihar ta yanke a ranar Alhamis dangane da taƙaddamar Masarautar Kano.

Babbar Kotun Tarayyar ta ce dokar da ta rushe masarautu a jihar na nan daram amma kuma ta soke aiwatar da dokar wadda gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi.

A lokacin yanke hukuncin, Mai Shari’a Abdullahi Muhammad Liman ya ce ba daidai ba ne gwamnan Kano ya aiwatar da dokar soke masarautun saboda akwai umurnin kotun da aka bayar da ya dakatar da duk wani yunkuri na gwamnan Kano wajen aiwatar da sabuwar dokar da ta cire rawanin sarakuna biyar a jihar ta Kano.

Mai shari’a Liman ya ce “A don haka na bayar da umurnin cewa dukkan matakan da gwamnati ta ɗauka na soke su amma hakan bai shafi sabuwar dokar masarautu ba. Amma sun shafi matakan da gwamna ya dauka ciki har da sanya hannu a sabuwar doka da kuma sake nada Sanusi..

Kotun ta ce “An soke dukkan matakan da masu kare kai a shari’ar suka ɗauka, amma kuma hakan bai shafi dokar ba.”

“Waɗanda ke kare kansu a shari’ar na sane da umurnin kotun duk da cewa ba a aika musu da kofin umurnin ba. Amma sun gani a kafafen soshiyal midiya, a don haka ba daidai bane su kawar da kai”, in ji Alkali Liman.

Mai shari’a Liman ya mayar da wannan ƙara zuwa wata Kotun Tarayyar karkashin mai shari’a Amobeda Simon amma har sai an kammala sauraren karar da ɓangaren gwamnati suka ɗaukaka.

A watan Mayun da ya gabata ne dai ’yan Majalisar Dokokin Kano suka yi ƙudirin dokar inda kuma ba tare da ɓata lokaci ba Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanya mata hannu ta zama doka.

Bisa dokar ne gwamnan ya rushe sarakunan biyar ciki har da Alhaji Aminu Ado Bayero ya kuma sake naɗa Muhammadu Sanusi II a matsayin sarki na 16, bayan da tsohon gwaman jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya tuɓe shi a 2020.

To sai dai kuma a ranar 23 ga watan na Mayu ne ɗaya daga cikin masu naɗa sarkin Kano, Alhaji Aminu Babba Ɗan Agundi mai sarautar Sarkin Dawaki Babba ya ƙalubalanci dokar a Babbar Kotun Tarayyar da ke Kano, inda ya nemi alƙalin da ya ayyana dokar a matsayin haramtacciya.

Wannan lamari na dambarwar masarautar Kano na ci gaba da ɗaukar hankali inda jama’a ke ci gaba da tofa albarkacin bakinsu.

Ko a yau Juma’a, duk sarakunan biyu sun yi zaman fada da halartar sallar Juma’a — inda Sarki Sanusi ya yi a babban Masallacin Kano da ke Babbar Fada, yayin da Sarki Aminu ya yi tasa tare da zaman fada a Nassawara.

Fitowar Sarki Sanusi II daga fada a yau Juma’a
Yadda Sarki Aminu ya yi zaman fada a yau Juma’a