✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dalilin da APC ta fadi zaben wasu jihohi a 2019 —Buhari

Mun tabbatar da jam’iyya ce da ke girmama zabin mutane.

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi bayani kan dalilin faduwar jam’iyyar APC a wasu daga cikin kujerun gwamnoni a zaben 2019.

Shugaba Buhari ya ce abu ne da ba a saba gani ba jam’iyya mai ci ta fadi wasu daga cikin kujerun gwamnoni, sai dai duk da hakan ta kasance ba don ta so ba kuma ta dauki dangana.

Ya yi wannan wajabi ne a fadar shi da ke Abuja lokacin da yake karbar Gwamna Ben Ayade na Jihar Cross River da kuma Gwamna Bello Matawalle Jihar Zamfara, wadanda a bayan nan suka sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.

Shugaba Buharin ya ce ’yan adawa sun lashe zaben jihohin wanda ya hakan manuniya ce ta cewa jam’iyyar APC tana girmama sakamakon zabe bisa ga ra’ayin daidaikun al’umma.

Gwamna Ayade da Matawalle sun samu rakiyar Shugaban Kwamitin Riko na Jam’iyyar APC, Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe, Shugaban Kungiyar Ci gaban Gwamnoni, Gwamna Atiku Bagudu na Jihar Kebbi da kuma takwaransa na Jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar.

“Ina taya ku murnar sauya sheka zuwa babbar jam’iyya. Mun fadi zaben gwamnonin jihohinku a baya wanda ba a saba gani ba amma mun tabbatar da mu jam’iyya ce da ke girmama zabin mutane.

“Muna kara jaddada cewar muna girmama mutanenmu shi yasa muke son a yi zabe na gaskiya da adalci kuma kowane Shugaba ya kamata ya kwantanta gaskiya da rike amanar mabiyansa.

“Ka zama jagora mai tsari da tabbatar da jajircewa a kan wannan tsarin hali ne me kyau da ya kamata ya wanzu a cikin al’ummarmu.

“Mutanenku za su ci gaba da girmamaku bayan wannan sauyin sheka da kuka yi zuwa APC a lokacin da kuka ra’ayi.

“Mun tabbatar ba wanda zai matsa muku, amma kuma da tabbaci cewa ta haka ne za ku iya taimakon mutanenku wajen ciyar da su gaba,” cewar Shugaba Buhari.

A cikin sanarwar da ta fito daga hannun mai magana da yawun Shugaban Kasa, Femi Adesina, ya ce Buhari ya yi alfahari da matakin da gwamnonin suka dauka na sauya shekar zuwa APC.

“Wannan wani lokaci ne na jin dadi da alfahari a tarihin wannan babbar jam’iyyar ta mu, saboda barin tsofaffin jam’iyyun a wannan lokacin na nuna karfin da jam’iyyar ke karawa a kullum.

Aminiya ta ruwaito cewa, Shugaba Buhari ya mika tuta ga gwamnonin sannan ya daga hannaynesu yana cewa APC jam’iyya ce mai daraja.

A nasa bangaren, Gwamna Mai Mala Buni, ya yi godiya ga Shugaba Buhari kan ayyukan ci gaba da ya ke kawo wa kasa, sannan ya kara da cewa za a yi babban taron gangamin jam’iyyar APC a watan Yuli, 2021.