✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilan kin saukowar kayan abinci duk da girbin da manoma suka yi

Kwararru a harkar noma sun bayyana cewa rashin kayan noma na zamani da samun takin zamani cikin sauki da kasuwannin sayar da kayan amfanin gona…

Kwararru a harkar noma sun bayyana cewa rashin kayan noma na zamani da samun takin zamani cikin sauki da kasuwannin sayar da kayan amfanin gona tare da rashin magance rikicin manoma da makiyaya na daga cikin manyan dalilan da suka sanya farashin kayan abinci ya ki saukowa duk da girbin da manoma suka yi.
Bayanan tashin farashin kayayyaki da Hukumar Kididdiga ta Kasa ta fitar sun nuna duk da watannin takwas din da aka yi ana samun raguwar farashin kaya, farashin kayan abinci ya ki saukowa.
A kwanannan mutane da dama sun koma noma don su goyi bayan shirin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari  na rage dogaro ga albarkatun mai, sakamakon haka an samu karuwar kayan abinci a kasuwannin kauyuka amma farashin kayan abincin kamar gero da shinkafa sun ki saukowa idan aka kwatanta da girbin da aka yi a baya.