✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilan da suka janyo nadin shugabannin ma’aikatu ya tsaya cik

Har yanzu Majalisar Dattawan Najeriya ba ta fara aiki a kan bukatar da Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar mata ba na amincewa da nade-naden da…

Har yanzu Majalisar Dattawan Najeriya ba ta fara aiki a kan bukatar da Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar mata ba na amincewa da nade-naden da ya yi na shugabannin ma’aikatun gwamnati ba.
Nadin da ya yi na kwanannan shi ne na mataimakin shugaban gwamnan babban bankin Najeriya na CBN da membobi hudu na kwamitin sa idon a kan harkokin kudi na babban bankin Najeriya.
A wasiku biyu da Buhari ya aike wa majalisar a ranar 12 ga watan Oktoban wannan shekara wacce mataimakin shugaban majalisar Ike Ekweremadu ya karanta a zaman majalisar, shugaban ya bukaci a amince da nadin Misis Aisha Ahmad a matsayin  mataimakiyar gwamnan babban bankin Najeriya da membobi hudu na kwamitin sa ido a kan harkokin kudi na bankin.