✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dalibi ya tsere daga hannun ‘yan bindiga a Filato

Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wasu dalibai biyu na makarantar Calvary International Ministry, da ke karamar hukumar Barkin Ladi a Jihar Fulato. Wakilinmu…

Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wasu dalibai biyu na makarantar Calvary International Ministry, da ke karamar hukumar Barkin Ladi a Jihar Fulato.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, daya daga cikin daliban da aka yi garkuwa da su, ya samu nasarar tserewa daga hannun ‘yan bindigar inda yanzu haka yana hannun Jami’an tsaro.

Rahotanni sun bayyana cewa, ‘yan bindigar sun kai hari makarantar ce da sanyin safiyar ranar Alhamis, inda kafin jami’an tsaro su ankara, tuni sun yi awon gaba da dalibai biyu kafin daya ya kubuta daga hannunsu.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Jihar Filato, Gabriel Ogaba, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Kawo yanzu, hukumar gudanarwar makarantar bata ce uffan ba kan lamarin

Makarantar wacce aka fi saninta da suna CAPRO, tana nan kilomita kadan daga babban filin sauka da tashin jiragen sama na kasa da kasa na Yakubu Gowon da ke yankin Haipang.