Wani dalibi mai kimanin shekaru 20 da haihuwa ya gurfana a gaban wata kotun yanki dake zamanta a Karu, Babban Birnin Tarayya Abuja bisa zargin garkuwa da budurwarsa.
Jami’an ‘yan sanda dai sun zargi matashin mazaunin yankin na Karu da sace budurwar tasa mai kimanin shekaru 16 da haihuwa da nufin yin lalata da ita.
- Ya yi garkuwa da ‘yar cikinsa yana neman kudin fansa daga matarsa
- ‘Yan bindiga sun kai hari masallaci, sun yi garkuwa da mutum 17
Dan sanda mai shigar da kara, Ayotunde Adeyanju ya shaidawa kotun cewa mahaifin yarinyar mai suna Balogun Kehinde ne ya kawo karar wanda ake zargin ga caji ofis din ‘yan sanda na Karu ranar shida ga watan Oktoban 2020.
Ayotunde ya ce wanda ake zargin ya sace yarinyar ne a watan Satumba.
Ya ce sai a ranar 18 ga watan Oktoba ne mahaifin yarinyar ya gano cewa matashin wanda yake ikirarin kasancewa saurayinta ne ya sace ta.
Mai shigar da karar ya ce a lokacin da ‘yan sanda ke gudanar da bincike, matashin ya amsa aikata laifin, ko da dai daga baya ya musanta aikatawa a gaban kotun.
Ayotunde ya ce laifin ya saba da tanade-tanaden sashe na 273 na kundin dokokin Penal Code.
Da yake yanke hukunci, alkalin kotun, mai shari’a Inuwa Maiwada ya amince ya bayar da matashin beli akan kudi N50,000 tare da mutum daya wanda zai tsaya masa.
Daga nan sai ya dage zaman kotun har zuwa ranar tara ga watan Nuwamba domin ci gaba da sauraron karar.