Bacin rana ta sa wani dalibi mai shekara biyar a duniya ya mutu a ruwa yayin darasin koyar da ninkaya da makarantarsu ta Redeemers da ke Ogba a Ikejan Jihar Legas ta shirya.
Dalibin, mai suna Chidera Eze, dai ya gamu da ajalinsa ne lokacin da malaman shi suka kai su wajen shakatawa na Ivory Health Club da ke unguwar ta Ikeja.
- Amurka za ta tallafa wa Najeriya da wasu kasashen Afirka 9 da $215m su yaki yunwa
- Na fi duk masu neman takarar Shugabancin Najeriya gogewa – Ameachi
Bayanai na nuni da cewa Chidera ya zame sannan ya fada cikin ruwan ne lokacin da suke tsaka da wasa tare sauran dalibai.
Da yake zantawa da manema labarai, mahaifin Chidera, mai suna Anthony ya yi zargin cewa malamai da ma’aikatan wajen ba ma su san dan nasa ya fada ruwan ba, har sai da ya mutu.
Ya ce, “Na kawo yarana makarantar ranar Litinin da safe, kafin daga bisani na wuce wajen aiki. Wajen misalin karfe 10:52 na safe, Shugabar makarantar, Misis Adeola Oladipo, ta kira ni a waya ta shaida min cewa dana ya yi hatsari kuma an garzaya da shi asibitin Ikeja
“Nan take na garzaya wajen, inda na iske gawar shi. Sai na tambayi malamar tasu abin da ya faru da shi, amma ta ce ita mabba ta sani ba.
“Sai na tambayi likitan, inda ya tabbatar min da cewa ba a kawo shi da rai ba.
“Na tambayi malamai da masu kula da su da ma masu aiki a wajen shakatawar, amma dukkansu suka gaza ba ni gamsasshen bayani.
“Ina tsaka da kuka ne sai matata ta shigo, ina kokarin yi mata rufa-rufa, sai ta shige asibitin. Daga nan na shiga dimuwa. Daga nan ne muka wuce ofishin ’yan sanda domin kai rahoto,” inji Anthony.
Mahaifin dalibin ya kuma yi ikirarin cewa wasu hotunan kyamarar tsaro ta CCTV sun nuna cewa dan nashi ya shafe sama da minti 30 bayan fadawa ruwan kafin ya mutu.
Ya ce daga karshe ma sai wani wanda ya zo wajen don yin ninkaya ne gano gawar ta shi.
Tuni dai hukumar makarantar ta sanar da rufe ta saboda iftila’in, har sai abin da hali ya yi.