✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalibar Firamaren da ta fi tsufa a duniya ta rasu

Ta rasu a kasar Kenya tana da shekara 99

Dalibar firamare mafi tsufa a duniya, Priscilla Sitienei, mai shekara 99, ta mutu.

A cewar wani jikanta, tsohuwar ta mutu ne bayan da ta soma nuna alamun rashin lafiya jim kadan bayan ta dawo daga makaranta a ranar Laraba, daga nan sai rai ya yi halinsa.

Priscilla ta shiga makarantar firamare ta Leaders Vision Prep School da ke garin Eldoret a Kenya a shekarar 2010, ta kuma soma karatun boko ka-in da na-in tare da yara jikokinta ‘yan shekara 12.

A hirarta da Hukumar kula da Ilimi da Al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya (UNESCO), Priscilla ta ce, ta koma makaranta ne domin ta nuna muhimmancin ilimi musamman ga iyaye yara mata domin su je makaranta.

“Ina so wannan ya zama abin misali ne ba gare su ba kawai, har ma da sauran yara mata na duniya da ba sa zuwa makaranta. Ilimi shi ne banbanci tsakaninka da kaza,” inji Priscilla.

Priscilla wacce aka fi sani da ‘Gogo’ wanda hakan ke nufin ‘kaka’ da harshen Kalenji, a hirarta da BBC a shekarar 2015, ta ce, ta yi murna da yanzu ta iya karatu da rubutu, damar da ba ta samu ba a baya.

Gogo ta mutu ne a lokacin da suke shirya-shiryen zana jarabawarsu ta gama firamare a mako mai zuwa