✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Daliban Zamfara 5 sun tsere daga hannun masu garkuwa

Yanzu saura Maliban Makarantar Kaya 69 a hannun masu garkuwar.

Mutum biyar daga cikin dalibai 74 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a garin Kaya na Jihar Zamrfara sun tsere daga hannun masu garkuwar.

Mahaifin daya daga cikin daliban da suka kubuta ya ce ’ya’yan nasu sun shaida musu cewa ’yan bindigar sun raba su gida biyu, kuma a lokacin da ake rarraba su ne mutum biyar daga cikinsu suka sulale.

  1. Dan bindigar da ya yi garkuwa da Daliban Afaka ya shiga hannu
  2. Daukar makami don kare kai laifi ne —Babban Hafsan Soji

Ya shaida wa Sashen Hausa na BBC cewa dan nasa ya dawo gida a galabaice da misalin karfe daya na dare, kafin wayewar garin Alhamis, amma a halin yanzu ana jinyar su a asibiti.

A ranar Laraba ’yan bindiga suka kutsa Makarantar Sakandaren Gwamnati da ke garin Kaya a Karamar Hukumar Maradun ta Jihar Zamfara, suka yi awon gaba da dalibai 74 da ke shirin rubuta jarabawa.

Maharan sun kuma yi awon gaba da malaman makarantar biyu, a harin da aka kai lokacin da dalibai kimanin 400 ke halartar makarantar.