Hajiya Karimatu Aminu Abubakar ita ce Shugabar Hukumar JAMB shiyyar Kano wacce ke kula da jihohin Kano da Jigawa da Katsina. A tattaunawarta da Aminiya ta bayyana cewa Hukumar JAMB ta fito da rubuta jarrabawa ta hanyar kwamfuta ne don ta magance dabi’ar nan ta magudin jarrabawa. Haka kuma ta musanta batun da ake yi cewa Hukumar JAMB ba ta da kyakkyawar alaka da jami’oi don haka ma ta kayyade musu yawan makin da za su dauki dalibai da shi, inda ta ce shugabanta ya bayar da dama ga kowace jami’a ta dauki dalibai bisa makin da take ganin ya yi daidai da tsarinta, da sauran batutuwa da suka shafi harkar ilimi gaba daya.
Tarihin rayuwa:
An haife ni a garin Kano. Na yi karatun firamare a makarantar firamare ta Magwan sannan na shiga Sakandaren ’Yan mata ta Dala duk a Jihar Kano. Bayan na kammala sai na tafi Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya inda na fara yin wani kwas na share fage, kafin daga bisani na samu gurbi a jami’ar inda na yi digiri a bangaren Zoology. Bayan na kammala sai na yi bautar kasa. Bayan na kammala sai na shiga harkar koyarwa, inda na koyar a makarantun sakandare daban-daban a Jihar Kano. Sai kuma a shekarar 2000 na sami aiki a Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Jami’a (JAMB) inda na fara a matsayin Principal Admin Officer. Haka muna tafe muna tafe har na kai ga wannan kujera ta Shugabar Hukumar ofishin shiyya wanda ya hada jihohin Kano da Jigawa da kuma Katsina.
Ayyukanta a Hukumar JAMB:
Hukumar JAMB tana iya kokarinta wajen ganin ta sama wa dalibai gurbin karatu a jami’o’in kasar nan tare da tabbatarwa jami’o’in sun bi ka’ida wajen daukar dalibai. Hukumar ba ta goyon bayan dabi’ar satar amsa shi ya sa ma a kullum take fito da sabbin tsare-tsare na rubuta jarrabawar. Ina iya tunawa a lokacin da ake rubuta jarrabawa a takarda da muka gano ana magudin jararbawa sai muka fito da hargitsa jarrabawar yadda za zama a aji guda amma daliban suna rubuta jarrabawa daban-daban. A yanzu ma da muka fara ta kwamfuta mutane sun yi zaton duk cibioyin da mutum ya y i rajista a nan zai rubuta jarrabawar don haka suka fara hada baki da masu cibiyoyin sai dai ba su sami hakan ba domin mun yi kokarin wargaza shirinsu ta hanyar canza tsarin, ma’ana mutum zai rubuta jarrabawa ne kawai a inda sunansa ya fito ba wurin da ya yi rajista ba. A yanzu haka ma da hukumarmu ta gano an yi magudin jarrabawa a wasu jihohin inda aka kama fiye da cibiyoyi fiye da 40 a fadin kasar nan. Yawanci ba su da masaniyar cewa an sanya kyamarori a wurin ba, don haka aka yi ta kama su. A yanzu haka ana duba yadda za a bullo wa lamarin a jarrabawa ta gaba don toshe duk wata kafa da za ta bayar da damar magudin jarrabawa. Manufarmu shi ne mu samar da sahihi kuma ingantaccen sakamako wanda jami’oi za su yi alfahari da samun dalibai masu hazaka amma ba masu magudin jarrabawa ba. Hakan ya sa a bana Hukumar ta shigo da malaman jami’oi inda suka kula da daliban a lokacin rubuta jarrabawar. Abin da nake cewa Hukumar ba ta goyon bayan magudin jarrabawa sai dai kamar yadda aka sani a ko’ina ba a rasa baragurbi to abin da yake kasancewa kenan amma ba wai ita hukumar da kanta ke bayar da damar magudin jarrabawa ba. Duk yadda ka kai da iyawarka sai ka samu wasu sun bata maka lamari. Muna fatan dai lokaci zai zo da wadanda ake hada bakin da su ake yin magudin jararbawa za su zo su daina su kuma dalibai su ma za su gane cewa cutarsu ake yi da hakan su ma su dawo su daina.
Batun da ake yi kuma na cewa Hukumar JAMB ta fitar wa jami’oi kayaddajen makin da za su dauki dalibai, wanann zance ba hala yake ba. lokacin da aka gama rubuta jarrabawa kamar yadda yake bisa tsarin aiki, Hukumar ta kira taron masu ruwa da tsaki inda ta bayyana cewa ta fitar da maki 120 ga jami’a, sai maki 100 kuma ga Kwalejojin limi da na fasaha. Amma kafin ta zartar da hakan sai da ta nemi amincewar dukkanin shugabannin jami’o’in akan hakan. Sannan kuma ta ba su damar su ma a nasu matakin za su iya sanya nasu makin daidai da tsarin jami’ar da kuma kwasakwasai. Alhamdulllah shugabanmu na yanzu kasancewarsa daya daga cikin amlaman jami’oin domin ya koyar a Jami’ar Ilorin tsawon shekaru 40 don haka akwai kyakkyawar alaka tsakaninsa da jami’oin.
Nasarorin da ta samu:
A gaskiya ni ban fiye tunanin cewa ina da wasu nasarori a rayuwa ba, ni dai kawai ina aikina da zuciya daya. Allah Ya sani ina son aikina ina kuma jin dadin yin sa. Kasancewar ni mutum ce mai son mu’amala da jama’a don haka ba na ganin aikina a matsayin matsala duba da yadda aikin yake na hulda da jama’a kai tsaye. A kullum ofis di na a bude yake ina sauraron jama’a da masu neman karin bayani da masu korafe-korafe tun daga kan dalibai har zuwa iyayensu.
kalubale:
Duk da cewa a rayuwa mutum bai rasa kalubale nan da nan, ni zan ce ba na fuskantar wani kalubale sosai a wajen aikina, idan ma akwai kalubale sai in ce bai wuce yadda matasanmu ba su son yin aiki mai yawa ba. ba su da juriyar aiki. sai ki ga da matashi ya fara aiki sai ya ajiye wai shi ya gaji. Ya fi son idan ya zo wajen aiki ya yi hirarsa ya tafi gida. A gaba daya abin da na lura da matasan wannan lokaci sun fi son cin bagas ma’ana suna son komai ya zo musu a sama ba tare da sun wahala ba. Haka kuma irin yanayin yadda tarbiyyar matasanmu ta gurbace abin yana damuna musamman yadda aka wayi gari matasanmu ba su girmama na gaba da su. Mu mun tashi da giramama na gaba da mu. Mun sani yaro ba ka raba shi da ‘yan fitintinu amma duk da haka a wancan lokacin muna shakkar malamanmu ba mu son yin abin da zai jawo mana rigima.
Yadda take ganin za a bunkasa harkar ilimi:
Lamarin ilimi abu biyu ne da wanda ya shafi malamai da kuma bangaren dalibai. Dole ne malamai su san cewa wannan aiki da suke yi taimakon al’umma ne wanda suke da sakamako mai girma a wurin Allah. Malamai su dage wajen koyar da dalibai su tabbatar mafi yawan daliban da ke ajin sun gane darasin kafin a dora. Sannan idan an zo jarrabawa su ji tsoron Allah wajen yi wa dalibai adalci. Mu a da malamanmu kokari suke su taimaka mana su ga mun ci jarrabawa. Suna da shaukin koyarwar a zuciyarsu ba irin malaman yanzu ba wadanda har shan alwashi suke yi sai sun kayar da dalibi a lokacin jarrabawa. Wanann ba daidia ba ne.
daliban yanzu ba su son karatu. Darasin da aka koya musu a makaranta ma ba su son yin bitarsa ballantana su je dakin karatu su zurfafa bincike ko kuma su rika daukar litattafai suna karantawa don amfanin kansu.
To ta yaya mutum zai ci jarrabawa? Sun riga sun kashe zuciyarsu da satar amsa. Sun dogara cewa ta hanayar satar amsa za su ci jarrabawa har ma kiran abin suke yi da taimako. Idan malamai suka matsa sai su ce ai ba su son a taimaka musu. Wai satar amsa ta zama taimako. A da muna yara babu abin da ke gabanmu sai karatun zalla kullum muna shaukin karatun tare da zuwan jarrabawa, babu ruwanmu da satar amsa. A gaskiya idan ana son gyara sai dalibai sun dage sun mayar da hankali ga karatuttukansu tare da yin bincike sannan a samu a kai ga gaci.
Iyalinta:
Na yi aure a shekarar 1982 a yanzu haka ina da ’ya’ya biyar, maza biyu mata uku. Babbansu a yanzu haka yana koyarwa a Kwalejin Kimiyya da Fasaha da ke Kaduna. Ya yi aure har da ’ya’yansa biyu. Akwai kuma wata macen da ta yi aure bayan ta yi digiri a fannin aikin jarida. Shi ma daya namjin yana karatun digirinsa a Jami’ar Northwest. Sai kuma ‘yar autata da ta ke matakin farko na digiri a Jami’ar Bayero.
Burinta:
Babban burina a rayuwa shi ne na samu na cika da imani yadda zan hadu da Allah lami lafiya. Ina kuma burin na ga al’umma ta koma kan tafarkin gaskiya.
Abin da take so a tuna ta da shi:
Ina so ko bayan raina a rika tunawa da ni a matsayin wacce ta bayar da gudummawa wajen taimaka wa al’umma.
Shawararta ga mata:
Ina shawartar mata da su dage wajen neman ilimi na addini da kuma na boko. Duk da cewa a yanzu mata sun fara fitowa amma akwai bukatar a
kara samun yawan mata masu ilimi. Ba lallai sai mutum ya yi aikin gwamnati ba. A fili yake rayuwar wanda ya yi ilimi da wanda bai yi ba ba daya ba ce, akalla idan mace ta yi ilimi za ta taimaka wa ’ya’yanta da karatunsu. Ilimin da take da shi zai ba ta damar sanin abin da ke faruwa a duniya ba za ta zauna a cikin jahilci ba.
Sannan akwai bukatar mata su dage wajen tarbiyyar ‘ya’yansu musamman a wannan lokaci da harkar fyade ta yi yawa. A wannan zamani dole ne iyaye su dage wajen sanya ido akan shigi da ficen ‘ya’yansu da kuma irin mutanen da suke mu’amala da su. Ya kamata a tashi gadan-gadan domin kawo karshen wanann dabi’a ta fyade. Dole ne sai an dage ana yin addu;a tare da sanya ido. Akwai bukatar mu tsaya mu gyara gidajnemu da tarbiyar ’ya’yanmu ba wai mu shige muna zancen gudajen wasu ba.