Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta tsare wasu dalibai su hudu ‘yan ajin karshe a Makarantar Horar da Jami’an ‘Yan Sanda ta Najeriya dake Wudil a jihar Kano.
Daliban dai wadanda ke karatun digiri a makarantar sun fada komar hukumar ne bayan an kama su da wani sunduki dake kunshe da wani sinadari da aka yi ittifaki miyagun kwayoyi ne a garin Kwanar Dangora dake karamar hukumar Kiru a jihar ta Kano lokacin da suke kokarin kai wa wani dillali kayan.
- NDLEA ta kama masu safarar miyagun kwayoyi 15 a Kaduna
- Za a yi ‘yan sandan da aka kashe a zanga-zangar #EndSARS karin girma
Kwamandan makarantar, AIG Zanna M. Ibrahim wanda ya tabbatar da hakan lokacin da yake jawabi ga sabbin dalibai da aka dauka ranar Alhamis ya kuma ce tuni suka fara bincike domin gano ko daliban na da hannu a zargin da ake musu ko kuma a’a.
Kazalika, ya ce makarantar ta kori karin wasu mutum 25 saboda rashin da’a da kuma karya dokokin makarantar., ciki har da wata mace da ta sami juna biyu ta hanyar da ba ta dace ba.
Daga nan sai kwamandan ya ja kunnen sabbin daliban kan bukatar yin da’a, yana mai cewa makarantar sam ba za ta lamunci kowanne irin nau’i na rashin da’a daga dalibai ba.
Zanna ya ce makarantar za ta bullo da gwajin kwayoyi da kuma na juna biyu ga dalibai a kai a kai domin tabbatar da cewa wadanda suka cancanta ne kawai ake dauka a makarantar.
Ya ce, “Mun sami wata daliba da juna biyu kuma tuni mun kore ta, saboda haka ba ma so a maimaita wannan kuskuren.
“Lokacin da daliban za su dawo hutu daga gida za mu tabbatar mun yi musu gwaji don tabbatar da cewa ba su da wata matsala kafin su ci gaba da karatunsu,” inji shugaban makaraantar.
Sama da dalibai 1,400 ne aka yi bikin rantsar da su daga tsangayoyi daban-daban na makarantar.