Jami’ar Jihar Kaduna (KASU) ta tabbatar cewa wasu dalibanta sun lakada wa wasu kananan hafsoshin soji da ke karatu a Jami’ar Soji ta NDA duka a kan wata budurwa.
Kura ta turnike tsakanin kananan sojojin da daliban ne a wurin bikin rantsar da sabbin daliban jami’ar da sojoin suka halarta ranar 12 ga watan Oktoba, 2021.
- Dubun masu damfara a ATM ta cika a Jigawa
- ’Yan ta’adda 13,243 da iyalansu sun mika wuya a Arewa maso Gabas – Sojoji
Da yake tabbatar da hakan a ranar Laraba, kakakin jami’ar KASU, Adamu Bargo, ya ce daliban sun kuma lalata motar sojojin, amma ya bayyana cewa an da dakatar da daliban da suka yi fada da sojojin.
“Lamarin ya faru ne a wajen bikin rantsar da sabbin dalibai, inda daya daga cikin kananan hafsoshin sojin ya yi kokarin karbar lambar wata daliba, amma ta ki.
“Wani dalibi ya shiga domin ya sulhunta lamarin, amma sai wani daga cikin sojojin ya tsinke shi da mari.
“Hakan ya sa sauran daliban da ke wurin suka yi wa sojojin taron dangi suka yi musu rubdugu da duwatsu da sanduna.
“Sojojin sun yi kokarin tserewa a cikin wata motarsu kirar Toyota Matrix, amma dalibai suka rufe kofar shiga jami’ar, sannan suka yi wa motar kaca-kaca.
“Daya daga cikin sojojin da bai samu ya shige cikin motar ba kuma dalibai sun ritsa shi, sun yi masa bugun tsiya,” a cewar Bargo.
Ya kara da cewar an fara gudanar da bincike kan lamarin, sannan za a dauki mataki kan daliban.
“Hukumar makaranta ba za ta lamunci duk wani nau’i na rashin da’a a wajen da ake koyon tarbiyya da halaye na gari ba,” kamar yadda ya bayyana.