✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Press To Play

Daliban Kankara na hanyar komawa gida —Gwamnatin Katsina

Kwamitin Tsaron Jihar ya tabbatar cewa an sako yara 340 da aka yi garkuwa da su

Kwamitin Tsaro na Jihar Katsina, ya ce daliban da aka yi garkuwa da su a makarantar sakandaren Gwamnati ta GSSS Kankara na kan hanyarsu ta zuwa gida bayan masu garkuwar sun sako su.

Shugaban Kwamitin Kuma Sakatare Gwamnatin Jihar, Mustapha  Inuwa, ya ce a ranar Alhamis da dare ne Gwamnatin Jihar ta amso yara 340 daga hannun masu garkuwar a Tsafe, Jihar Zamfara mai makwabtaka da Jihar Katsina.

Babban Daraktan Yada Labarai na Gwamna Masari, Abdu Labaran tare da Mai Bai wa Gwamnan Shawara ta Kafofin Sadarwar Zamani, Abdulhadi Bawa sun ce an ceto yaran ne bayan shiga tsakani da Shugaban Kungiyar Meyetti Allah na Kasa, Alhaji Muhammad Hardo Kiru ya yi.

Daliban da aka ceto a motar da za ta kai su Katsina

Sun ce daliban da ke hanyarsu ta dawowa Jihar Katsina sun samu rakiyar masu shiga tsakani, jami’an tsaro domin dawo da su.

Wani bidiyo da ke yawo ya nuna yaran a cike da farin ciki a bayan wata babbar mota da dare a hanyarsu ta komawa Katsina.

Ana sa ran kawo su Gidan Gwamnatin Jihar su gana da Masari, yayin da aka yi masu masauki a sansanin alhazai inda ake sa ran Shugaba Buhari zai gan su kafin ya tashi zuwa Abuja bayan gama wani gajeren hutun da ya yi a gidansa da ke Daura.

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter a daren bayan samun labarin sakin yaran, Buhari ya ce: “Na yi murnar samun labarin sakin daliban GSSS Kankara da aka yi garkuwa da su.

“Wannan babban kwanciyar hankali ga daukacin Najeriya da ma duniya; Najeriya na matukar godiya ga Gwamna Masari, Hukumomin Tara Bayanan Sirri da kuma sojoji da ’yan sanda.”

Buhari a lokacin da ake sanar da shi ta waya cewa an karbo daliban

Kishin-kishin din sako Daliban Kankara

Ranar Alhamis Gamayyar Kungiyoyin Arewa (CNG) ta janye zanga-zangar da ta shirya a Jihar Katsina ne naman a ceto daliban; ta ce ta janye ne saboda gamsuwa da bayanan da gwamantin ta yi mata cewa ta yi nisa a kokarinta na ganin masu garkuwar sun saki yaran.

Labarin sakin daliban na zuwa ne bayan yan sa’o’i da gwamnatin jihar ta karyata labarin sako su da Hadimar Shugaban Kasa, Abiki Dabiri-Erewa ta wallafa cewa an sako yara 333.

A ranar Alhamis din ce kuma kungiyar Boko Haram ta fitar da bidiyon da ta nuna yaran da ta ce daliban makarantar ne, domin tabbatar da cewa suna hannunta.

A ranar Juma’a da dare ne ’yan bindigar da suka musayar wuta da jami’an ‘yan sanda da ke tsaron makarantar suka yi awon gaba da daruruwan daliban.

Daga baya kungiyar Boko Haram ta yi ikirarin yin karkuwa da su, har ta fitar da bidiyon da wani daga cikin daliban ke neman gwamnatin Tarayya ta cece su, ta kuma biya bukatun kungiyar.

Gabanin haka Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Masari, ya watsi da ikirarin da Boko Haram ta yi da farko cewa ita ce ta dauke yaran.
Wasu daga cikin daliban da suka ce ba za su bar makarantar ba sai an karbo yaran

Takaddar bidiyon Boko Haram na farko

Bidiyon na biyu ya fito ne washegarin ran da Masari da Rundunar Tsaro ta Najeriya suka karyata ikirarin kungiyar na sace da daliban.

Kakakin Rundunar Tsaro, Manjo Janar, John Enenche ya ce ikirarin da na Boko Haram farfaganda ce kawai; kuma rundunar ta aiki don ceto daliban cikin aminci.

Shi kuma Masari cewa ya yi a iya saninsu masu garkuwa da mutane ne suka dauke yaran.

Jihar Katsina na daga cikin jihohin da suka fi fama da matsalar garkuwa da mutane a Najeriya.

Ya kara da cewa an gano yaran suna ajiye ne a ‘dajin Zamfara’, ana kuma tattaunawa da masu garkuwar kan sako daliban.