Tun bayan raba Jihar Sakkwato da cire wasu jihohi daga cikin ta kamar Zamfara da Kebbi da Neja da sauran su an kafa wata qungiya da ake kira da suna SOKEZA,wato Sakkwato, Kebbi, Zamfara, Ita wannan qungiyar an samar da ita ne domin hada kan mutanen wadannan jihohin duk da kasancewa ba jiha daya ake ba.
Wannan qungiyar ta SOKEZA ta samar da ci gaba mai dimbin yawa tsakanin wadannan jihohin musamman ga dalibai,
A 2012 gwamnatin Jihar Sakkwato ta gina jami’a mallakar ta, Kuma tana ba da gurbin karatu mai yawa ga ’yan jihohin Kebbi da Zamfara, Kuma la’akari da wancan qungiya ta SOKEZA gwamnatin jihar ta ga yiwuwar sanya kudin makaranta su zama iri guda tsakanin al’ummar wadannan jihohin, Wato babu bambanci tsakanin wanda ya fito daga Zamfara Da Kebbi da wanda ya zo daga Sakkwato. Ita ma gwamnatin jihar Kebbi lokacin da ta bude jami’ar Kimiya da fasaha da ke garin Aleiru ta sanya dokar kowane dan jihar Sakkwato ko Zamfara kudi iri daya zai biya da yadda ’yan jihar Kebbi za su biya!
Wannan taimakon da mutanen SOKEZA ke yi wa kan su ya taimaka matuqa musamman ga daliban Jihar Zamfara, domin a lokacin baya babu jami’a a Zamfara sai a 2013 sannan tsohon Shugaban qasa Goodluck Jonathan ya gina, duk da haka bai hana ’yan Jihar Zamfara neman gurbin karatu a jami’ar Jihar Sakkwato ba, Sai dai bayan kammalar hutun shekara da Hukumar jami’ar ta Sakkwato ta bai wa dalibai, Sai ga wata sabuwa ta bayyana!
Hukumar jami’ar Sakkwato ta bayyana cewa ‘daga yanzu duk wanda ba dan Jihar Sakkwato ba, zai riqa biyan kudin makaranta daidai, ma’ ana an cire rangwamen da aka yi wa ’yan jihohin Kebbi da Zamfara.
A baya kowane dalibi daga SOKEZA yana biyan qasa ga Naira dubu 50, Sai dai yanzu ’yan jihohin Zamfara da Kebbi za su biya kusan Naira dubu 100! Wato an samu qarin kudin makaranta da ake kira registration har na Naira dubu 60!
Don haka daliban jihar Zamfara suke kira ga gwamnatin jihar, da mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, da sauran Shuwagabanin masu ruwa da tsaki a harkar ilmi da su yi mai yiwuwa domin ganin a taimake su, ko dai a rage masu kudin a maida su kamar yadda suke a farko, ko kuma a rage masu wani abu daga kudin. Dalilin da ya sa daliban jihar Zamfara da ke karatu a jami’ar jihar Sakkwato suka fi mayar da hankali kan a taimake su shi ne, Ita gwamnatin jihar Kebbi ta bi sahun maganar inda nan take gwamnan jihar Alhaji Atiku Bagudu ya yi alqawarin ci gaba da biyan kudin makarantar ga daliban jihar da ke karatu a jami’ar ta Sakkwato.
Duk da tura saqonnin kuka da daliban jihar Zamfara ke yi ga gwamnatin jihar amma babu wani hobbasa da suka ga an yi!
A yanzu haka akwai dimbin daliban jihar da suka yi alqawarin barin karatun domin ba su da halin biyan wadannan kudi, Wasu kuma sun yi alqawarin barin makarantar su ma dai domin rashin hali na biyan kudin!
Sanin kowane idan har matashi ya fara karatu a jami’a kuma ya bari, to tabbas abu ne mai wahala bai zama matsala ga al’umma, Kuma duk matasan nan yanzu ne yakamata a ba su tallafin da yakamata domin su mori qasar nan a gaba, da arewa baki daya.
Ko a lokacin baya da daliban Kebbi da Zamfara na biyan qasa ga dubu 50, ba kowa ne ke da halin biyan kudin cikin lokaci ba.
Da fatan gwamnatin jihar Zamfara da mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III da dukkan manyan magabata na yankin SOKEZA da arewa baki daya, su yi duba da idon basira kan wannan matsalar mai girman gaske ga arewacin Najeriya.
Ibrahim Rabilu Tsafe Alzamfari, Jihar Zamfara, 07064282182