Wasu daliban Islamiyya sun rasu a sakamakon wani hatsarin kwalekwale a Karamar Hukumar Bagwai ta Jihar Kano.
Akalla dalibai 20 ne ake fargabar sun rasu bayan kifewar kwalekwalen a kan hanyarsu ta zuwa wani taron Mauludi ranar Talata.
- ‘Hatsarin kwale-kwale ya kashe ’yan Najeriya sama da 400 a wata 16’
- Mutum 50 sun mutu a hatsarin jirgin ruwa
“Yanzu da muke magana, ana ci gaba da aikin ceto, kuma jami’anmu sun gano gawarwaki 20 an kuma yi nasarar ceto wasu mutum bakwai da ransu,” inji kakakin Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Kano, Saminu Abdullahi da misalin karfe 9.15 na dare ranar Talata.
Majiyarmu a Babban Asibitin Bagwai ta ce an kai gawarwaki 20 asibitin bayan kifewar kwalekwalen da ke dauke da mutum sama da 40.
Ta ce kwalekwalen ya yi hatsari ne da misalin karfe 4.30 na yamma a yayin da yake dauke da daliban makarantar Madinatu Islamiyya da ke kauyen Badau tare da sauran fasinjojin a kan hanyarsu ta zuwa garin Bagwai.