Hedikwatar Tsaro ta Najeriya (DHQ) da ke birnin Abuja, ta ce dakarun sojoji da sauran hukumomin tsaro na ci gaba da fadi-tashi don tabbatar da kubutar da daliban da aka sace a Makarantar Sakandaren Kimiyya ta Gwamnati da ke Karamar Hukumar Kankara a jihar Katsina.
Babban Jami’in kula da harkokin sadarwa na hedikwatar, Manjo Janar John Enenche ya tabbatar da hakan yayin yi wa manema labarai karin haske ranar Laraba a birnin Abuja dangane da ayyukan dakaru a kan lamarin sace daliban.
- Kudin makamai: Kotu ta soke daurin da aka yi wa Olisa Metuh
- An yi ’yar jefe-jefe da hanjin aladu a zauren Majalisar Taiwan
- Rashin tsaro: Kungiyar Izala ta umarci limamai su yi Alkunut
Enenche ya ce sojoji sun samu dukkanin wasu bayanai da suka kamata daga hukumomin tsaro da kuma gwamnatin jihar Katsina dangane da duk wata harkalla ta sace daliban da aka yi.
Sai dai ya ce babban kalubalen da hukumomin tsaro ke fuskanta a yanzu shi ne tabbatar da kubutar da daliban cikin aminci.
Dangane da batun tattaunarwa da gwamnatin jihar ta yi da wadanda suka sace daliban, Manjo Enenche ya ce sojoji ba su da wata alaka da tattaunawar, lamarin da ya ce iko ne kadai da ya ta’allaka da gwamnan jihar.
Ya ba da tabbacin cewa a yayin da gwamnatin jihar ke ci gaba da taka rawar gani a nata bangaren, hukumomin tsaro sun dukufa wajen ganin an ceto daliban wadanda dukkaninsu na raye.
Manjo Enenche ya yi watsi da ikirarin da shugaban kungiyar masu tayar da kayar Boko Haram Abubakar Shekau ya yi na alhakin sace daliban, lamarin da ya misalta a matsayin farfaganda da kungiyar ’yan ta’addan ta saba yi.
Ya ce sojin kasar na ci gaba da samun nasarori a kan ’yan ta’adda a yankin Arewa maso Gabashin kasar da kuma ’yan bindiga a yankin Arewa maso Yamma musamman a makonnin biyun da suka gabata.