✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalibai 270 sun fafata a gasar Musabakar Fikihu ta farko a Jihar Jigawa

Kimanin dalibai 270 masana ilimin fikihu suka fafata a gasar Musabakar Fikihu ta farko da Hukumar Ilimi ta Jihar Jigawa ta shirya, kamar yadda ake…

Kimanin dalibai 270 masana ilimin fikihu suka fafata a gasar Musabakar Fikihu ta farko da Hukumar Ilimi ta Jihar Jigawa ta shirya, kamar yadda ake fafata gasar karatun Alkur’ani da ake yi a matakin kananan hukumomi da jihohi da kuma kasa.

Babban Sakataren Hukumar Ilimin Addinin Musulunci ta Jihar Jigawa Malam Yakubu Abbas Yakubu ya ce gwamnatin jihar ta dauki wannan mataki ne da nufin sanya al’ummar jihar su dage wajen neman ilimin fikihu da sauran fannonin ilimin addinin Musulunci domin inganta rayuwar al’ummar jihar.

Da yake jawabi a madadin Kwamishinar ilimi, Babban Sakataren Ma’aikatar Ilimi ta Jihar, Malam Abdullahi Hudu ya ce kananan hukumomin 27 ne jihar ne suka shiga Musabakar Fikihu karo na farko inda kowace karamar hukuma ta ba da wakilai 10, biyar maza biyar mata, wato dalibai 270 suka halarci Musabakar. 

Sai ya hori matasa su tashi tsaye wajen neman ilimin addini musamman fikihu domin ba a bauta wa Allah sai da ilimi, saboda Allah Ya ce a nemi ilimi kafin a bauta maSa, don haka ibada ba ta yiwuwa sai da sanin Allah da kuma sanin yadda ake yi ibadar.  Ya ce sarakuna ne suka nemi a fara yin Musabakar Fikihun domin yin ta yana da alfanu sosai, kuma za ta taimaka wajen zaburar da matasa su nemi ilimin da za su bauta wa Allah. Malam Abdullahi Hudu ya ce gasar wadda aka fara a bana da alamun za ta yi tasiri ganin yadda jama’a suka rungumi gasar hannu bibbiyu.

An fafata gasar ce a matakai uku; ’yan shekara  16 zuwa 18 da ’yan shekara 19 zuwa 23 da kuma ’yan shekara 23 zuwa 25.

A yayin gasar karamar Hukumar Kafin Hausa ce ta zo ta daya da maki 19 da rabi sai karamar Hukumar Birniwa ta zo ta biyu da maki 17 yayin da karamar Hukumar Birnin Kudu ta zo ta uku da maki 16 da rabi. Kuma wadanda suka yi nasara a gasar an ba su kyaututtuka, inda mata suka samu na’urorin firiji maza kuma aka ba su na’urorin kwamfuta ’yar yawo, sauran wadanda suka shiga gasar kuma gwamnatin jihar ta bai wa kowanensu shadda yadi biyar-biyar, mata kuma aka ba su atamfofi a matsayin karramawa.

Alkalin Musabakar Alhaji Bala Musa Kazaure, ya ce a ajin ’yan shekara 16 zuwa 18, karamar Hukumar Jahun ce ta yi nasara, sai kuma ajin ’yan shekara 19 zuwa 23 karamar Hukumar Kaugama ce ta yi nasara sai karamar Hukumar Kafin Hausa ta yi nasarar lashe gasar gaba daya wato ajin ’yan shekara 23 zuwa shekara 25.

A jawabin Mai martaba Sarkin Dutse Alhaji Nuhu Muhammed Sunusi ya hori matasa su dage wajen neman ilimin addini, kuma ya bukaci gwamnatin jihar ta fadada gasar zuwa mataki-mataki kamar yadda gasar Alkur ani take da ajujuwa shida domin jama’a da dama su samu shiga. 

Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Badaru Abubakar, wanda Mataimakinsa Alhaji Ibrahim Hassan Hadeja ya wakilta a wajen rufe Musabakar, ya ce gwamnatin jihar ta bullo da Musabakar Ilimin ce saboda akwai Musabakar Alkur’ani da ake yi a duniya domin yin ta yana da muhimmanci watakila idan gasar ta samu karbuwa za a iya fadada ta ta zama gasa ta duniya a nan gaba.

Ya shawarci matasa su dage wajen neman ilimi musamman na addini domin ba a bauta wa Allah sai da ilimi.