An wallafa bidiyon wani otal da ke karkashin ruwa wanda ya jawo muhawara a shafukan sada zumunta na zamani.
Shi dai wannan otel shi ne babban otal na farko a karkashin ruwa a duniya.
- Masu garkuwa da mutane sun bukaci ‘Maltina’ a matsayin fansa
- ‘Ba don karba-karba ba, da sai Arewa ta shekara 300 tana mulki’
An ruwaito cewa, ana biyan Shiling miliyan 5.5 na kasar Kenya (kimanin Naira miliyan 22) duk daki guda da ke otal din a kowane dare.
Babban otal din Muraka na karkashin ruwa shi ne irinsa na farko a duniya kuma ya kunshi wani yanki na tsibirin Maldibes Rangali Island Resort wanda ke cikin kasar Maldibes ta Kudancin nahiyar Asiya.
Conrad Maldibes ne ya yada bidiyon a kafar Instagram tare da daukar daya daga cikin manyan dakunan kwana na otal din da ke karkashin teku mai nisan kafa 16 a Tekun Indiya.
A wannan gini mai ban sha’awa akwai wurin wanka mai zaman kansa. Daya daga cikin manyan dakunan yana dauke da bandaki da kuma dakin barci.
Kimanin masu ziyara 360 na iya zuwa don kallon tekun Indiya. Wata da ta kalli bidiyon mai adireshin @lobewoluofficial ta yi sharhi, inda ta ce: “Mene ce manufar ziyartar otel din. Idan ni da abokin zamana mun ziyarci otal din, me zai sauya mu? Tunanin wannan wuri kadai zai iya sanya zuciya ta karaya.”
Wata kuwa mai adireshin @mama_dino ta ce: “Ba da ni ba, ba zan taba tunanin wani zai kai ni wannan wuri domin ya burge ni ba. Don haka, ba abin gwaninta ba ne a wurina”.