Dakin karatu da littattafai ta Ni’ima wanda ake kira a turance ‘Pleasant library and book club’ da ke cikin garin Katsina ya shirya taron bita a dakin taro na Jami’ar Al-kalam domin wayar da kai tare da fadakarwa a kan muhimmancin sanin makamar aiki dangane da sana’o’in da suka daukin nauyin koya wa matasa mata 130 kafin bikin yaye su.
Shugaba, kuma mu’assasin dakin karatum, wanda kuma tsohon Sakataren hukumar tara rarar kudin man fetur ne ta kasa PTDF, Injiniya Muttaka Rabe Darma ya ce “Babban makasudin yin wannan taron bita shi ne a ilmantar da wadannan matasa da suka kammala koyon sana’o’i domin su san yadda za su rika gudanar da sana’o’in da makamantansu. Ba koyar da mutun wani aiki kadai ke da muhimmanci ba, sanin yadda zai tafiyar da aikin shi ne babban abin lura da kuma mayar da hankali.” Inji shi.
An gayyato masana daban-daban da suka gabatar da jawabai a wajen wannan taron bita. Sai dai kuma Injiniya Muttaka ya nuna damuwarsa kan rashin halartar wasu mutane tare da bankunan da aka gayyato “Duk wani reshen banki da ke cikin garin Katsina babu wanda bamu gayyata ba, kuma sun amsa cewa za su zo, amma abin takaici babu dayan da ya turo wakilinsa bayan kuma ba kudi muka ce su bamu ba.Kazalika.
“Kullum mabukata karuwa suke yi, saboda haka wajibi ne mu fito mu taimaki ‘ya’yanmu, kannanmu da jikokinmu da abin da za su rika dogaro da shi, maimakon yawan maula wadda a karshe ake fadawa ta’addanci,” inji Injiniya Muttaka.
Ita dai wannan dakin karatu ta ‘Pleasant Library and book club’ ta dauki nauyin koyarwa matasa 800 da suka hada da maza da mata,wadda kuma shi Injiniya ya dauki nauyin biyan kudin duk abin da ake bukata na bayar da wannan horo.
Kamar yadda Aminiya ta samu labari, an fara yin yekuwar neman masu son shiga wannan shiri ba kuma tare da anyi la’akari da yanki ko shiyya ba, an kuma bayar da takardun shiga kyauta ga masu so. Sannan aka dauka mutun 800 a matakin farko a inda kuma mata ne suka fi yawa. Ganin haka ne yasa aka fara dauko mata 130 domin farawa da su a matakin farko.
Mata 80 ne suka koyi saka, 30 suka koyi Komfuta da kuma 20 wadanda suka koyi abinci. Mafi yawan wadanda Aminiya ta tuntuba sun nuna farin cikinsu akan wannan nasara da suka samu, sannan su ka ja hankalin ‘yan-uwansu da su zage damtse wajen koyon sana’a.