A ranar Larabar makon jiya ce Ministan Ilimi Malam Adamu Adamu ya sanar da cewa babu makarantar Gwamnatin Tarayya da za ta shiga jarabawar ta WAEC ta bana.
Amma a farkon makon nan ya sake yin bayani, inda ya ce matakin da suka dauka bai shafi makarantun gwamnatocin jihohi da makarantu masu zaman kansu ba, wanda hakan ke nufin jihohi da makarantun kudi za su iya rubuta jarabawar idan sun cika ka’idojin da aka shar’anta.
Tuni wasu jihohin suka fara shirye-shiryen dawowa makaranta domin shirin fara jarabawar, wadda aka ce za a fara a watan Agusta, kafin a dakatar.
Wannan batun na Ministan ya jefa mutane musamman iyaye da dalibai cikin rudu da damuwa, musamman kasancewar batun ya zo ne bayan Minista a Ma’aikatar Ilimi Emeka Nwajuiba ya dandana wa mutane batun, inda ya ce dalibai da suke aji shida na firamare da aji ukun sakandare da aji shida za su dawo makaranta domin rubuta jarabawa.
Iyaye da dalibai da malaman makarantu da Aminiya ta zanta da su sun bayyana cewa sun ji zafin dage jarrabawar.
Iyayen sun bayyana bacin ransu a kan yadda gwamnati ta yi amai ta lashe a kan dakatar da dalibai jarabawar kammala makaranta, wanda da sakamakon ne, mutum ke samun damar shiga jam’ia da kwalejojin ilimi da sauransu.
Ba mu ji dadin dage jarabawar ba – Iyayen dalibai
Shugaban Kwamitin Iyayen dalibai na Makarantar Tunawa da Garba Gere da ke Bauchi Alhaji Nuhu Sani ya ce “da farko mun yi murna da muka ji za a fara jarrabawar a ranar 4 ga Agusta, sai kuma muka ji murnarmu ta koma ciki, da aka dage saboda yin haka zai kashe kwarin gwiwa ga yaran da suke karatu.
“Da aka ce an sa ranar fara jarabawar, sai suka koma karatu gadan-gadan amma da aka daga sai suka koma wasannin da suke yi da ba makaranta.
“Mun yi zaton gwamnati za ta yi wani tsari kamar sauran kasashe, domin dalibanmu su yi jarabawa, kamar yadda wasu kasashe suka yi amma kuma sai ga shi an dakatar”.
Shi ma Malam Mummuni Maikwai ya ce dansa ba ya daga cikin wadanda Gwamnatin Jihar Bauchi ta ce za ta biya wa jarabawar WAEC, da yaron ya ga haka sai ya yi ta yin dako da talla har Allah Ya ba shi kudin da ya biya jarabawar da burin sai ya ci wannan jarabawa, “dage wannan jarabawa ya girgiza dukkanmu, saboda yin haka ya dakushe masa kwazonsa.”
Mummuni ya ce abin tsoro shi ne rufe makarantu da aka yi, “muna gani shi ya kara jawo zaman banza a tsakanin yara wadanda ba su da tarbiyya a cikinsu da suka rasa abin yi, shi ne aka samu karuwar yawan fyade da sace-sace da aikata laifuffuka daban-daban”.
A Maiduguri, Malam Abubakar Bulama, ya ce hakika hakan bai dace ba, “bayan kulle makarantu na dogon lokaci yara suna zaman gida, kwatsam kuma muna murnar za a ba da dama ga yaranmu a kan su samu damar rubuta jarabawa, sai muka ji wai an hana kuma babu ranar da za a gudanar.
“To ka ga wannan ba karamin lamari ba ne, ko me ake ciki kamata ya yi a duba rayuwar yaran nan, don su ne manyan gobe.
“Ni ina ganin a sake tunani wajen daukar matakin da aka yi, domin yi wa yaran nan adalci”.
Ita ma wata mahaifiyar wani dalibi da Aminiya ta zanta da ita a Maiduguri, Hajiya Chilla Bukar ta bayyana takaicinta da ta ji an hana dalibai rubuta jarabawa.
Ta ce wannan rashin tausayi ne, “bayan yara sun shafe wata hudu babu wani abu, duk karatun da yaro ya yi ya tafi, domin haka ina roko ga gwamnati da ta sake tunani, ta kyale ’ya’yanmu su sami damar rubuta jarabawarsu”.
Shi ma Ustaz Ahmad Ali Albani, malami da ke koyarwa a makarantar firamare da sakandare ta Independence Acadamy a Ibadan.
Ya ce, “Batun dakatar da jarabawar WAEC a matsayina na malamin makaranta kuma daya daga cikin iyayen yara, ban ji dadin yadda mahukunta suka dage jarabawar ba, bayan tun farko sun tabbatar da cewa za a yi.
Dalili shi ne mafi yawancin daliban suna la’akari da yanayin yawan shekarunsu da yadda za su kare karatunsu a gaba da suke ganin dakatar da yin jarabawar ya zama koma-baya ga rayuwarsu.
“Mu ma iyaye muna da irin wannan tunani na bakin cikin dakatarwar da muke hangen koma baya ne ga ’ya’yanmu, bayan mun kashe kudaden makaranta.
Ya kamata gwamnati ta yi waiwaye. Kamata ya yi a tanadi dukkan nau’in kariya daga cutar ga daliban domin samun saukin yin jarabawa cikin walwala”.
Shi ma Joseph Akande, wani mahaifi a Ibadan cewa ya yi “na yi bakin ciki da jin labarin dakatar da jarabawar nan amma ba abin da zan ce sai rokon mahukunta su yi mana adalci”.
Kehinde Adesokan cewa ta yi “ka san matsalarmu a Najeriya yanzu haka wasu suna nan suna yin amfani da wannan dama wajen cuwa-cuwar cika aljihunsu ta haramtacciyar hanya. Dole mu yi hakuri da irin wannan tafiya da ba-gaba-ba-baya”.
A taimaka mana kada a bata mana tsarin rayuwa – dalibai
Yusuf Bashir da Maryam Kolo, daliban ajin karshe a Maiduguri, sun bayyana mamakinsu na jin wannan labari.
“Da farko mun yi murna sosai da muka ji cewar za mu koma makaranta don rubuta jarabawa amma kwatsam sai kuma suka sake jin wani labari sabanin haka.
A gaskiya ba karamin kaduwa muka yi ba,” inji Yusuf, inda ya kara da cewar idan har za a bude kasuwa da wajen shakatawa, bai ga dalilin da zai hana a ce su ba za kyale su, su rubuta jarabawa ba.
“A tuna fa wannan jarabawa tana da muhimmanci ga duk wani dalibi, kuma ita ce tushen gina rayuwarmu matasa, don da ita ce za ka gina ci gaban rauwarka na kasancewa abin da za ka zama a rayuwa, walau likita, ko injiniya, ko aikin jarida, karantarwa da sauransu”.
An bata min tsari.
Maryam Kolo a nata bangaren ta ce an cuci rayuwarsu kuma an kusan lalata mata burinta na yadda ta tsara rayuwarta.
Ta ce “ka ga ban wuce shekara 16 ba amma na tsara yadda rayuwa za ta tafi da ikon Allah, amma kawai sai ga shi an kawo min tarnaki a ciki, na so a ce shekarar nan na samun shiga jami’a, wanda har na yi jarabawar share fagen shiga jami’a.
“Ina da burin in zama likita. Ni dai rokona ga gwamnati don girman Allah ta sake duba lamarin”.
Sai mun kara shekara guda ke nan?
Wani dalibi Mukhtar Ahmad ya ce “wata bakwai na yi ina yin karatu don in ci wannan jarabawa amma kwatsam sai ga shi gwamnati ta daga wannan abu, bai yi mana dadi ba.
“Cunkoson da ake yi a kasuwanni ya fi cunkoson da ake yi a makarantu. Ya kamata gwamnati ta duba wannan lamari.”
Mukhtar ya ce yanzu idan ba a duba lamarin ba, “sai mun kara shekara guda ke nan kafin mu ce za mu je jami’a”, inji shi.
Sannan ya shawarci ’yan uwansa da su rika karatu da neman sana’a a gida domin samun madogara.
Yawancinmu mun ma manta darussan.
Wata daliba mai suna Fatimat Muhammed a Ibadan cewa ta yi “da yawa daga cikinmu ba mu yi bitar karatu a cikin gidaje na tsawon lokacin da aka rufe makarantu ba.
“Saboda haka ko an kyale mu yi jarabawar WAEC a yanzu to akwai dalibai da yawa da za su fadi, ba za su ci jarabawar ba domin kwakwalwarsu ta manta da irin abubuwan da aka koya musu a baya kafin rufe makarantun”.
Wata daliba a Jihar Kaduna, Khadija Muhammad Ango ta bayyana cewa wannan matakin da gwamnati ta dauka bai mata dadi ba, kasancewar dage jarabawar zai bata mata lissafi.
“Ni da nake tunanin kammala sakandare bana, domin na tsara shakerun da nake son in kammala karatuna, sannan in samu miji in yi aure.
“Amma irin wannan matakan za su iya jawo wa mutum tsaiko. Mu dai ga mu ga Allah nan. Amma idan akwai hali ina kira ga gwamnati da ta sake duba lamarin nan.
“Za a iya rubuta jawabawar nan kashi-kashi idan ba a so mu cakude ne. Sai misali mutum 100 su rubuta jarabawa da safe, wasu 100 su rubuta da rana wasu da yamma.
“A tunanina, wannan ba matsala ba ce. Amma an hana mu jarabawa, amma su kuma suna tarukan siyasa, mu kuma muna zuwa kasuwanni da sauransu”.
Ba Najeriya kadai ce ke yin jarabawarmu ba – WAEC
A nata bangaren, Hukumar WAEC ta ce ba za ta yanke hukunci ba kai tsaye yanzu, inda ta ce kasashe biyar ne suke rubuta jarabawarta, ba Najeriya ce kadai ba.
A tattaunawarsa da jaridar Premium Times, Shugaban Ofishin WAEC na Najeriya (HNO) Patrick Areghan ya ce suna ci gaba da nazari a kan matakin.
“Yanzu dai ba za mu yanke ba kai tsaye. Kasashe biyar ne ke jarabawar, sannan muna aiki tare da hadin gwiwar gwamnati ne. Gwamnati na da damar daukar mataki irin wannan kuma ba za mu iya hanawa ba”.
A shirye muke mu yi jarabawar WAEC – Makarantun kudi
A nasa jawabin, Shugaban kungiyar Masu Makarantu Masu Zaman Kansu (NAPPS), Yomi Otubela ya ce a shirye suke su bi dokoki da ka’adojin Hukumar NCDC wajen rubuta jarabawar.
Shugaban kungiyar ya bayyana hakan ne a wata zantawa da jaridar Premium Times, inda ya ce maimakon a dakatar da jarabawar baki daya, gara a ba da dokokin da za a bi wajen rubuta jarabawar.
“Mun yi amannar cewa dukkan makarantu masu zaman kansu sun shirya rubuta jarabawar WAEC. Mun riga mun bi duk dukkan matakan da suka dace domin kariya kamar yadda Hukumar NCDC ta bayyana”.
Za mu jira abin da gwamnati za ta ce – JAMB
A nata jawabin, Hukumar JAMB ta ce za ta jira abin da gwamnati za ta ce ba a karshen lamari game da batun dakatar da jarabawar.
Kakakin hukumar, Dokta Fabian Benjamin ne ya bayyana haka a lokacin da Aminiya ta tuntube shi domin jin ta hukumar kan makomar dalibai da suka rubuta jarabawar JAMB, ba su rubuta SSCE ba.
Ya ce hukumar na ba da dama a rubuta JAMB ba tare da SSCE ba, inda ya ce amma ba za su ba mutum damar shiga jami’a ko makarantar gaba ba, sai da shaidar kammala sakandare.
Wannan rashin tunani ne – Masana
Malam Aliyu Suleiman masanin ilimi mai sharhi a kan al’amura daga Jam’iar Maiduguri ya shaida wa Aminiya cewa sam babu tunani a kan wannan mataki da gwamnati ta dauka na hana daliban rubuta jarabawar, “don ni ban ga wani dalili ba na yin hakan.
“Idan ana maganar kare lafiyarsu, to ai sai a samar da matakan kariya a duk wuraren da za a yi jarabawar.
“Mene ne tunanin da gwamnati take yi, ta bude kasuwanni, ga bankuna ga guraren taron biki duk jama’a na haduwa, amma sai a batun ci gaban rayuwar matasa sannan za a ce wai ba za a amince su rubuta jarabawar karshe ba?
“Ni a shawarata, kamata ya yi a ba wa yaran dama su rubuta jarabawar, idan an ce ba a son cunkuso ai muna da manyan dakunan daukar karatu, kamar yanzu a nan Jam’iar Maiduguri muna da MPH, da yawa da ko da dalibai daya-daya za a saka a kowacce kujera za su wadatar.
“Ga na sauran manyan makarantu. Idan har kasar Nijar za ta bude makarantu, ga Shugaban Amurka Trump na kokarin a bude makarantu a Amurka, to babu wani dalili da zai hana a ba wa yaran nan damar su rubuta jarabawa.
“Mu ba mu ce a bude makarantu duka ba, amma su wadanda suke ajin karshe din ya kamata a tausaya musu”.
Wani mai sharhi kan al’amuran yau da kullum a Jihar Bauchi Kwamred Abdulahi Buba ya ce dage jarabawar zai sa da wuya yara su ci gaba da yin karatu har zuwa 2021.
Ya ce abin da ya faru ya sa shi kuka a kan tsarin ilimi na Najeriya da ma daliban makarantunmu baki daya.
Ya ce abin ya zama kamar ta leko ta koma ne ga iyaye da dalibai da kuma malamai saboda malamai suna gani dama ta samu.
“Masu makarantu dama sun durkushe, komawar ce damar farfadowa sai aka ce an fasa, a yanzu dole ne iyaye su zage damtse su ninka kwazonsu don ganin yaransu suna yin karatu, in ba haka ba samun nasarar jarabawar ko badi ne sai ikon Allah.”