Dakarun Rundunar Hadin Gwiwa ta Kasa da Kasa (MNJTF) na Jamhuriyar Nijar sun samu nasarar kashe gommai na mayakan ISWAP a wani hari da suka kai kan maboyar su da ke Arewa maso Gabashin Tafkin Chadi.
An ruwaito cewa sojojin sun kai farmaki kan maboyar ’yan ta’addan ne a cikin kuryar kauyen Ndaurori, wani gari mai iyaka da Najeriya da Jamhuriyar Nijar.
- Rasha ta hana ’yan jaridar Birtaniya 29 shiga kasarta
- Fursuna ya tsere daga kurkuku ta hanyar shigar mata
Wata majiyar leken asiri ce ta shaida wa Zagazola Makama, wani masani kan yaki da tayar da kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a tafkin Chadi.
A cewarta, an kashe mayakan da ba a tabbatar da adadinsu ba a yayin da wasu suka gudu da raunukan harsashi a jikin su.
Majiyar ta kara da cewa, harin da dakarun suka kai ya tilastawa ’yan ta’addan da suka tsere neman wurin buya a garin Bulabulin mai tazarar kilomita 28 daga Damasak.
Kazalika, majiyar ta ce mayakan na amfani da maboyar da suka fake domin kula da ’yan uwansu da suka jikkata.