Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya bayyana amincewarsa da nadin da aka yi wa tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanuri II a matsayin Khalifan Darikar Tijjaniyya a Najeriya.
Fitaccen shehin Darikar ya nuna farin cikinsa game da nadin ne a lokacin ziyara da Khalifan ya kai masa a gidansa da ke Bauchi, ya gabatar masa ta takardar shaidar nadin da aka yi masa daga Kaulaha a matsayin Khaflian Darikar a Najeriya.
- Yadda ’yan kabilar Ibo ke ganin tasku saboda sun musulunta
- Budurwa ta fada rijiya a Kano
- Kano: An bude makarantun da aka rufe saboda matsalar tsaro
“Ina farin ciki da zabin ka da aka yi a matsayin jagora kuma ina addu’ar Allah Ya yi maka jagora, Ya kare ka a sabon matsayin naka,” inji Sheikh Dahiru Bauchi.
Ya shawarci Khalifan Sanusi kar ya bari abokansa da wasu makusantansa su yi mummunan tasari a kan sabon matsayinsa na jagoran Darikar Tijjaniyya, saboda matsayi ne na addini wanda ba ya son a cakuda shi da siyasa ko harkokin kasuwanci.
Kada El-Rufai ya sake ya zo gidana
Tun da farko a jawabin nasa, Sheikh Dahiru Bauchi ya nuna fushinsa da Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai (abokin Sanusi), kan samamen da jami’an Gwamnatin Jihar suka yi a gidansa.
Shehin ya bayyana samamen da cewa fito-na-fito ne da Alkur’ani da kuma cin fuska a gareshi, saboda bai aikata wani abin da ya cancanci a yi masa hakan ba.
“Ina El-Rufai yake? Na zaci zai kasance daga cikin ’yan rakiyarka, da na umarci masu gadi kar su bari ya yi ko da taku daya habar wannan gidan, saboda shi ne ya tura da jami’an tsaro suka far wa daliban Alkur’ani da karfe 2 na dare a gidana,” inji Sheikh Dahiru Bauchi.
Idan ba a manta ba, jami’an Gwamnatin Kaduna sun taba kai samame a gidan malamin da ke unguwar Tudun Wada, Kaduna, inda suka yi awon gaba da almajiran da ke gidan, bisa zargin cewa tara su a wurin ya saba dokar kariyar COVID-19.
Ya ce, “Sun shigo gidana suna harba hayaki mai sanya hawaye suna tursasa wa wadanda ke ciki saboda kawai masu karatun Alkur’ani ne.
“Sun yi ta bin almajiran a guje, aka kai su wani wuri nesa da gari aka yi watsi da su.
“Har yanzu yawancin wadanda abin ya rutsa da su ba a san inda suke ba,” inji malamin.
Khalifa Sanusi ya nema wa El-Rufai gafara
A kan haka ne Khalifa Sanusi II ya roki Sheikh Dahiru Bauchi ya yafe wa El-Rufai kan abin da ya faru tare da fatan ba za a maimaita irin hakan ba.
A cewarsa, El-Rufai bai san abin da ya faru ba saboda, “El-Rufai ba ya Najeriya lokacin da abin ya faru, ni ma ba na kasar lokacin da abin ya faru.
“Ina so na tabbatar muku da cewa hakan ba za ta sake faruwa ba. Ina roko a madadinsa a matsayina na abokinsa.”
“Ina rokon ka da kar ka sa abin da ya faru a zuciyarka, idan ba haka ba karshen ba zai yi kyau ba. Babu mai son a lissafa shi a matsayin makiyi ga bayin Allah irinka. Don Allah ka yafe masa.”