✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dagewa da ibada cikin watan Ramadan da kuma bayansa

Zuwa ga ‘yan’uwa Musulmi, Wannan tunatarwa ce ga ni kaina da kuma sauran Musulmi. Ganin cewa muna cikin watan Ramadan, wanda daya ne daga cikin…

Zuwa ga ‘yan’uwa Musulmi,

Wannan tunatarwa ce ga ni kaina da kuma sauran Musulmi.

Ganin cewa muna cikin watan Ramadan, wanda daya ne daga cikin watannin da suka fi soyuwa ga Allah (SWT) kamar yadda Annabi Yusuf (AS) yake mafi soyuwa ga mahaifinsa a tsakanin sauran ‘ya’yansa.

Haka kuma wata ne wanda a cikinsa Musulmi a fadin duniya suke kara kaimi wajen yin ayyukan ibada tare da kara tuna Allah (SWT).

Tunatarwa

Wannan tunatarwa ce da ya kamata mu yi aiki da ita ba wai kawai a cikin watan Ramadan ba, har ma a  sauran watanni idan har Allah ya ba mu tsawon rai da yardarSa.

Ya zama tilas mu ci gaba da bauta maSa tare da ambatonSa domin wannan shi ne dalilin da ya sa ya halicce mu, kamar yadda ya fada: ” Kuma ban halicci mutum da aljan ba face don su bauta miNi.” (Al-Kur’ani Surah ta 51:56).

Wannan na nufin tsaida sallolin farilla da kuma yin nafiloli bakin gwargwadon iyawarmu, yin zikiri safe da maraice da kuma bayan mun gama salloli.

Don haka halin da muke ciki na hana taruwa a masallatai don yin jam’i saboda gudun yaduwar annobar COVID-19, kada ya hana mu ci gaba da gabatar da sallolin nan a gidajenmu tare da iyalanmu.

Domin idan muka yi su a gidan ma za mu samu cikakkiyar lada da yardar Allah.

Yawaita Addu’a

Mu ci gaba da yawaita addu’a, muna masu neman gafararSa a kan laifukan da muka yi masa da wadanda muka yi wa bayinSa.

Mu dage da neman gafarSa a kan zunubban da muka aikata wadanda muka sani da ma wadanda bamu Sani ba; da kuma wadanda muka yi a sarari da na boye, domin Shi Allah, Shi ne Al-Ghafur Ar-Rahim, Mai gafara Mai jin kai.

Haka kuma ya zama wajibi mu nuna godiyarmu ga Allah a kan ni’imomin da Ya yi mana da kuma wadanda Ya yi wa masoyanmu, domin fadarSa, “Idan kuka kasance masu godiya zan kara maku”.

Don haka kada mu gajiya wajen nuna godiyarmu a gare Shi.

Watan Alfarma

Watan Ramadan wata ne mai alfarma, domin a cikinsa ne aka saukar da Al-Kur’ani wanda ya kasance shiriya ga dan-Adam. Don haka mu yawaita karanta Al-Kur’ani tare da kokarin aikata abin da muka karanta a rayuwarmu ta yau da kullum.

Haka kuma mu yawaita yin ayyukan ibada don kara kusanci ga Mahalicinmu.

Ya dace mu rinka daurewa muna yin sahur, domin dimbin ladar dake tare da yinsa.

Haka kuma kada mu manta da yin addu’a yayin bude baki, mu roƙi bukatunmu gare Shi, domin Shi Mai amsa kiran bayinSa ne a kowane lokaci.

Ramadan wata ne da yake zuwa da rahamomin Allah masu dimbin yawa, don haka ya kamata mu dukufa wajen samun wannan garabasa.

Kada a shantake

Kada mu kasance muna shantakewa da barci, har sai lokacin sahur ya yi sannan mu tashi mu ci abinci kamar wadanda ba su san me suke yi ba. Kamata ya yi mu dage da tsayuwa don neman yardarSa da kuma kusanci zuwa gare Shi. Domin a koda yaushe muka neme Shi Yana nan, Ya fi kusanci da mu a kan majinaciyarmu. Don haka mu kara azama ta yin abin da ya sa aka halitta mu, ta hanyar kara kusanci a gare Shi. Ta haka sai Allah Ya taimake mu.

Mu kara dagewa da ayyukan kwarai cikin wannan wata na Ramadan, kada mu manta da yi wa al’ummar masoyin Allah kuma manzonSa (SAW) addu’a.

Mu yi ta kiran sunayen Allah kyawawa don neman rahamarSa da yardarSa a nan duniya da Lahira, tare da addu’ar samun shiga Aljanna madaukakiya tare da masoyanmu.

Yawaita azkar da salatin Annabi

Haka kuma mu yi wa duniya baki daya addu’a ta samun waraka, mu yi wa marasa lafiya da masu fama da talauci da batattau addu’ar samun waraka da shiriya.

Mu yawaita yi wa Annabi salati da kuma tawassuli da sunayen Allah kyawawa don samun karbuwar add’o’inmu.

Ina addu’ar Allah Ya ba mu ikon rike cikinmu da kuma inganta ruhinmu. Allah Ka ba mu dauriyar yafiya da kuma damar tuba zuwa Gare Ka.

Allah Ka sa azumin ya zame mana wani horo na samun dauriya ga dukkan kalubalen da za mu ci karo da shi na rayuwa ta yadda za mu ci gaba da neman AljannarSa har zuwa ranar komawarmu gare Shi da yardarSa.