✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

dage zabe ya kara wa APC karfi da damar karbe mulki daga PDP – dan Sarauniya

Jagoran Matasan Jam’iyyar APC, (APC Youth banguard) Injiniya Mu’azu Magaji Dawakin Tofa (dan Sarauniya) ya ce dage zaben da aka yi ya kara wa jam’iyyarsu…

Jagoran Matasan Jam’iyyar APC, (APC Youth banguard) Injiniya Mu’azu Magaji Dawakin Tofa (dan Sarauniya) ya ce dage zaben da aka yi ya kara wa jam’iyyarsu ta APC karfi da damar karbe shugabancin kasar nan daga hannun Jam’iyyar PDP, kamar yadda ya bayyana wa wakilinmu:

Aminiya: Injiniya kai ne jagoran matasan Jam’iyyar APC wato APC Youth banguard, kuma an ji kun yi shiru, ba kwa cewa komai wajen tallata jam’iyyarku ta APC, ko akwai wani abu da kuke yi a bayan fage na tallata ’yan takararku na matakai daban-daban?
Mu’azu Magaji: Gaskiya wannan tambaya tana da muhimmanci musammam yadda aka san mu da bayyana sahihancin jam’iyyarmu ta APC a Jihar Kano da kasa baki daya. Shirun da ake cewa mun yi ba wai mun daina aikin jam’iyya ba ne, muna aiki fiye da wanda muka yi a baya kafin a fitar da ’yan takara na neman shugabanci da wakilci a majalisun dokoki zuwa ta wakilai da sanatoci da gwamnoni da kuma Shugaban kasa. Wannan aiki da muke yi ya kawo bunkasar jam’iyya da tallata ’yan takararmu, kuma ko shakka babu muna ganin Jam’iyyar APC za ta samu nasara mai yawan gaske a Jihar Kano da kasa baki daya domin duk wanda ya ga irin magoya bayan da ke cikin jam’iyyar zai yarda cewa APC za ta samu gagarumar nasara da yardar Allah.
Aminiya: Me za ka ce game da dage zaben da aka yi?
Mu’azu Magaji: Babu shakka dage zaben da aka yi ya zamo mana alheri a fadin kasar nan domin idan ka duba za ka ga cewa jam’iyyarmu ta APC ta kara karfi ta kara samun goyon bayan al’ummar kasar nan ta kowace fuska domin kawo canji mai amfani a kasarmu mai albarka, sabanin yadda tun farko aka shirya za a gudanar cikin watan jiya. Sannan mun yi amfani da dage zaben wajen tsara wata gidauniya ta tallafa wa dan takararmu na Shugaban kasa, Janar Muhammadu Buhari inda muka kafa asusun da muka kira “Asusun Tallafa wa Buhari sakamakon dage zabe,” ko asusun ’yanci. Maimakon mu matasa mu yi fushi da dage zaben, sai muka ce duk matashi mai kishin Jam’iyyar APC ya rika sanya Naira 100 duk mako har zuwa mako shidan da aka kara domin a tara wasu kudi a kuma ci gaba da taimaka wa Janar Buhari wajen yakin neman zabe, kuma alhamdulillahi al’ummar kasa sun yi matukar kokari musamman matasa suna ba da Naira 100 duk mako, yanzu haka asusun na da kudi mai yawa. Hakan da muka yi ya sanyaya zukatan matasan kasar nan dangane da dage zaben, sannan mun bullo da wata hanya ta kara hade kan matasa ta yadda za su ci gaba da gudanar da harkokinsu na siyasa cikin natsuwa da sanin ya kamata a mtsayinmu na manyan wata rana.
Aminiya: Ta yaya kuka fara tunanin kafa wannan asusu?
Mu’azu Magaji: Ka san aiki irin na al’amuran matasa na bukatar shawarwari da tuntubar masu hangen nesa da sanin ya kamata. Don haka sai da muka yi zaman tattaunawa a ofishin yakin neman zaben Janar Buhari da ke Abuja da dukkan wakilan matasa 36 na jihohin kasar nan inda muka zartar da cewa za mu yi amfani da dage zaben domin tara Naira dari-dari duk mako don ba da gudunmawa ga yakin zaben Janar Buhari. Kuma a gaskiya matasa sun yi kokari matuka wajen ganin asusun ya samu taimako daga matasa kuma har yanzu suna bada Naira dari-dari duk mako a duk jihohin kasar nan. Sannan wani abin sha’awa, matasan sun yi na’am da wannan kokari namu wajen kawar da radadin dage zaben daga zukatansu kuma mun ga tasirin wannan aiki da muka yi.
Aminiya: Idan muka dawo Jihar Kano, yaya kuke kallon batun yakin neman zabe tsakanin manyan jam’iyyun da suke da karfi a jihar?
Mu’azu Magaji: To, ka san siyasar Jihar Kano tana da matukar bambanci da sauran jihohi, amma dai na lura ana yakin neman zabe babu hamayya mai karfi, inda nake kallon abin tamkar lami. Idan ka waiwayi baya ai ana hamayya da gogayya tsakanin ’yan takara a kowane mataki, sabanin yadda abin yake a yanzu babu wata gasar neman kuri’a mai tsauri.
Sannan ina jinjina wa Mai girma Gwamnan Jihar Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso saboda kokarin da ya yi na gudanar da muhimman ayyuka a jiharmu, tare da kawo managarcin canji a al’amuran jagorancin al’umma. Kuma ina nanata cewa matasan Jam’iyyar APC reshen Jihar Kano muna goyon bayan takararsa ta Sanatan Kano ta Tsakiya domin ingancinsa a shugabancin al’umma, kuma mun gamsu da dukkan ’yan takarar da jam’iyya ta baiwa damar yin takara a karkashinta domin kawo ci gaban jiharmu.
Aminiya: Mene ne sakonka ga matasan kasar nan wajen ganin sun gudanar da harkokin siyasa?
Mu’azu Magaji: A matsayina na matashi kuma jagoran kungiyar matasan Jam’iyyar APC, ina kira ga matasan kasar nan, su guji yin duk wani abu da ka iya jawo fitina walau wajen yakin neman zabe ko lokutan zabe ko bayan zabe, domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya. Zaman lafiya yana wuyan kowa, domin kowa na son kwanciyar hankali a wannan kasa. Ina tabbatar wa daukacin al’ummar kasar nan cewa da yardar Allah za a samu canji mai amfani idan Allah Ya bai wa jam’iyyarmu ta APC nasara a zaben da za a gudanar ranar 28 ga Maris da 11 ga Afrilu. Ina kira ga ’yan Najeriya su zabi Jam’iyyar APC domin ita ce take da manufofi kyawawa da kowane dan kasa zai ji dadin gwamnati.