More Podcasts
A tsakanin Hausawa, sunaye masu alaƙa da harshen Larabci sun kusan maye gurbin na gargajiya irin su Tanko da Talle da Audi da dai sauransu.
A da sunayen da Hausawa kan sanya wa ’ya’yansu na Annabawa ne ko Sahabbai ko mashahuran malaman Muslunci ne, amma yanzu iyaye kan aro wasu kalmomi su rika kiran ’ya’yansu da su.
Shin mene ne dalilin hakan, daga ina ya samo asali, kuma mene ne tasirinsa a al’adance da ma a addinance?
- NAJERIYA A YAU: Amfanin Komawa Makaranta A Ranar Da Aka Bude Bayan Hutu
- DAGA LARABA: Abin da ya sa matan wannan zamani ke ƙin auten talaka
Amsoshin waɗannan da ma wasu tambayoyi makamantansu shirin Daga Laraba na wannan makon zai binciko
Domin sauke shirin, latsa nan