✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

DAGA LARABA: Me ya sa ‘yan siyasa ke kin yarda da shan kaye a zabe?

Me ya sa 'yan siyasa ke irin wannan dabi'a duk lokacin da suka yi rashin nasara?

More Podcasts

Domin sauke shirin kai tsaye, latsa nan

A tsarin zabe, dole a samu wanda ya yi nasara, a kuma samu wanda ya fadi. Amma wannan ka’ida har yanzu ba ta samu wurin zama ba a fagen siyasar Najeriya, don kuwa da yawa daga cikin wadanda suka fadi ba sa yarda su rungumi kaddara, sai kaji suna kiran “Magudi aka yi, amma ni na ci zabe”.

Mene ne dalilin da ‘yan siyasar Najeriya ke  kin karbar kaddarar faduwa?

Saurari shirin Daga Laraba domin jin dalilin ‘yan siyasa na kirkirar wannan dabi’a ta kin karbar kaye a matsayin kaddara da ke shafa wa Najeriya bakin fenti a idanun duniya.