✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

DAGA LARABA: Kamen ’Yan Arewa: Shin Lokacin Daina Ci-Rani Ya Yi?

Shin Amotekun halastacciyar kungiya ce kuma tana da harumin tsare ’yan Najeriya haka kawai?

More Podcasts

Domin sauke shirin, latsa nan

’Yan Arewacin Najeriya akalla 200 ne ke tsare a hannun jami’an tsaron yankin Kudu maso Yammcin Najeriya (Amotekun), cikinsu har da fasinjoji 19 da suka shafe wata 10 a tsare.

Shin Amotekun halastacciyar kungiya ce a Najeriya kuma tana da harumin tsare ’yan kasar haka kawai?

A shirin namu na yau, za ku ji halin da ’yan Arewa da Aamotekun ta tsare suke ciki da matsayin doka a kan kungiyar da kamen da ta yi da kuma yadda za a shawo kan lamarin.

Ku latsa nan domin sauke shirin a wayoyinku ko kwamfutocinku domin sauraro a duk lokacin da ku ke bukata.