More Podcasts
Cin goro yakan zama jiki ga wadanda suka saba ta yadda ba sa iya dainawa cikin sauki.
Yawanci dattawa a Arewacin Najeriya har ma matasa suna cin goro, har yakan zame musu jiki, baya ga yadda ake amfani da shi a wajen tarukan daurin aure ko radin suna, duk da ba yankin ake noman shi ba.
- Tsadar Rayuwa: ‘Ba Mu Da Zarafin Bayar Da Kyautar Kirsimeti A Wannan Shekara’
- DAGA LARABA: Muhimmancin Barin Wasiyya Tun Kana Da Rai
A yankin Kudu da ake noma goro ma, yana da muhimmanci musamman ma ga kabilar Igbo.
Shirin Daga Laraba na wannan makon ya duba dalilin da masu cin goro ba su iya dainawa da kuma abin da masana suka ce zai iya faruwa idan cin sa ya yi yawa.
Domin sauke shirin, latsa nan