✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Daga biki

Wani barawo ne ya sato kyalla mai gemu, ya biyo gindin kuka sai ya ga ’yan banga. Ya tabbata kama shi za su yi, sai…

Wani barawo ne ya sato kyalla mai gemu, ya biyo gindin kuka sai ya ga ’yan banga. Ya tabbata kama shi za su yi, sai ya yi wuf ya goya akuyar nan, ya sa riga ya daure ta; ya nufo wurinsu. Suna haskawa sai suka ga mutum goye da akuya, sai suka daka masa tsawa, suka ce: “Daga ina?” barawo ya nuna katuwar kuka ya ce: “Dag buki muke can gidan, ni da jinjira mai cin kai.” Haba, sai duk suka watse!

Daga Amiru Isa, 08075959086