✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

dabi zai zabi Ronaldo a matsayin Gwarzon dan kwallon Duniyiya

Tsohon dan kwallon FC Barcelona da ke Sifen dabi ya ce ya canja shawara kuma ya amince zai kada wa shahrarren dan kwallon kulob din…

Tsohon dan kwallon FC Barcelona da ke Sifen dabi ya ce ya canja shawara kuma ya amince zai kada wa shahrarren dan kwallon kulob din Real Madrid da ke Sifen Cristiano Ronaldo kuri’a don ya kasance Gwarzon dan kwallon Duniya a karo na hudu.
Ya ce duk da yake ya fi amincewa da Lionel Messi na FC Barcelona a matsayin wanda ya fi cancantar lashe gasar, amma ganin yadda Ronaldo ya samu nasarar lashe Kofin Zakarun Turai (Champions League) da Kofin Nahiyar Turai (Euro) a kakar wasan da ta wuce ya sa shi yanke shawarar kada wa Ronaldo kuri’a don lashe gasar  maimakon Lionel Messi.
Idan za a tuna, dabi da Ronaldo dai sun yi cacar baki a kwanakin baya, bayan dabi ya goranta wa Ronaldo cewa Messi ya fi cancanta ya zama Gwarzon dan kwallon Duniya a karo na 6 amma Ronaldo ya mayar masa da martani cewa dabi ya nuna kyautar da ya taba lashewa ta Gwarzon dan kwallon Duniya a tarihin kwallonsa. Wannan gori da Ronaldo ya yi wa dabi ta sa wadansu ke ganin bai dace ba. Daga baya ne dabi ya canja shawara inda ya amince ya zabi Ronaldo a watan Janairun 2017 a lokacin da za a yi gasar.
’Yan kwallo uku ne suke fafatawa a gasar a duk shekara inda ake zabar na farko a matsayin Gwarzon dan kwallon Duniya.