✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dabbobin banza su mutu don…!

Wata macece za ta tafi aikin Hajji, sai ta ce wa mijinta ya kula da dabbonta da take kiwo. Da za su yi ban ban…

Wata macece za ta tafi aikin Hajji, sai ta ce wa mijinta ya kula da dabbonta da take kiwo. Da za su yi ban ban kwana ta ce masa: “Isa ka kula da dabbobina!” Bayan sun isa filin jirgi ta sake cewa masa: “Isa ka kula da dabbobina!” Bayan ta shiga jirgi ta sake lekowa ta ce: “Isa ka fa kula da dabbobina!” Wani mutum yana ji, sai ya ce masa akwai wurin mutum daya je ka hau. Bayan mako sai suka hadu a Harami, sai ta ce, “Wannan kamar Isa, kamar ta yi yawa.” Suka kuma hadu a wurin jifar Shaidan, sai ta ce: “Ko Isa ne?” Sai ya ce: “Ni ne!”Ta ce: “Wa ya kawo ka nan, kuma ina dabbobina?” Sai ya ce: “Dabbobin banza, sum utu don ubansu.”
Daga Anisa Abdullahi Adamu Daura, 07067716102