✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yaki da ta’addanci: Buhari na neman sojoji su canza salo

Buhari ya bukaci sojoji da su sauya dabarun yaki da ta'addanci.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, a ranar Talata ya umarci rundunar sojin Najeriya da ta sauya dabarun yaki da ta’addanci da sauran matsalolin tsaro da ke tunkurar kasar nan.

Shugaban ya bada umarnin ne a Abuja yayin taron laccar da aka gabatar a ranar Sojojin Najeriya (NADCEL) ta 2021, ta bakin Ministan Tsaro, Manjo-Janar Bashir Magashi (Mai ritaya).

  1. An kama ’yan Boko Haram biyu da maganin karfin maza a Borno
  2. Buhari ya umarci a gaggauta ceto duk daliban da aka sace

Buhari ya kuma nanata cewa yana sane da irin kalubalen da ’yan Najeriya ke fuskanta ta fannin tsaro.

Ya ce harkokin gwamnati da na kasuwanci sun fara dawowa daidai, bayan da ayyukan ta’addanci suka nakasa su tsawon lokaci, musamman a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

Shugaba Buhari, ya ce, “Ina yin kira ga Hafsoshin Tsaron Najeriya da su zage damtse da himma wajen kirkirar sabbin dabaru, na samun nasara a zukatan mutane da tunaninsu a halin da ake ciki yanzu.”

Kazalika, ya ce Rundunar Sojin Najeriya ta cancanci yabo kan yadda take yaki a ta’addanci a fadin kasar nan.

A cewarsa, “Saboda haka, a yayin da muke murnar nasarar da sojojin Najeriya da dukkan hukumomin tsaro suke samu, zan so in gode wa duk ’yan Najeriya masu kyakkyawar niyya kan nuna goyon baya da fahimtarsu.

“A matsayinmu na gwamnati mai rikon amana, muna sane da irin kalubalen da ’yan kasa ke fuskanta.

“Ina so in baku tabbacin cewa za a warware wadannan matsaloli cikin kankanin lokaci,” inji Buhari.