Na yawaita samun sakonnin da ke neman karin bayani a kan yadda za a rubuta kirkirarren labari, hakan ya sanya a wannan makon zan yi cikakken bayani kan dabarun rubuta kirkirarren labari.
Kafin a kai ga rubuta kirkirarren labari, ya zama dole marubuci ya samu jigon labari mai karfi, sannan ya zabi salo mai jan hankali, sannan ya zabi fuskar da zai ba da labarin, wato labarin zai kasance mai fuska daya ne, ko mai fuskoki da dama. Labari mai fuska daya zai kasance marubucin kamar shi ne jarumin littafin, zai kasance kamar labarin a kansa ya faru. Za a rika amfani da ‘ni’ ko ‘na’ ko ‘mini’ da sauransu a labarin. Misali, “Ban san lokacin da numfashina ya dauke ba. ‘Na kalle su’, ‘Ya yi mini kallo wulakanci, ‘Da ni kake magana?’ da sauransu.”
Fuska ta biyu kuma zai kasance marubucin ne yake bayar da labarin wani ko wadansu, wato ana amfani da fuskoki masu yawa.
Ya zama dole idan ana so a rike masu karatu sai marubuci ya nuna gwanintar harshe, zai iya hakan ne ta hanyar amfani da kalmomi masu dadin karantawa, ko ta hanyar amfani da tagwayen kalmomi wadanda ma’anoninsu suka bambanta, sannan ana so ya rika amfani karin magana ko amfani da siffatau kai-tsaye (Personafication) ko siffatau mai-kama (Simile) da sauransu don kara wa labarinsa armashi.
Ya zama dole marubuci ya san ka’idojin rubutu (Orthography), hakan zai sanya a fahimci sakon da yake son isarwa, ba tare an canja ma’anar jimlar da ya gina a labarinsa ba. Ma’ana ta hanyar yin amfani da Alamar Motsin Rai (!) ne, za a gane jimlar da ya gina a labarinsa ta shafi razana, mamaki ko sosuwar rai ne. Ta hanyar alamar Tambaya (?) za a fahimci marubuci tambaya ya yi. Don haka ya zama dole marubuci ya rika amfani da ka’idojin rubutu yayin ginin labarinsa.
Yana da matukar amfani marubuci ya fahimci muhimmancin raba da kuma hada kalmomi, ta haka ne zai fitar da asalin ma’anar kowace jimla da ya gina a labarinsa. Misali: 1 Ya kamata. 2 Ya kama ta. Jimla ta 1 tana nuna abin da ya dace. Jimla ta 2, tana nufin an cafke ta.
Marubuci ya fahimci yawan aron kalmomi daga wani harshe daban kamar Turanci da Faransanci da sauransu za su wahalar da masu karatu, za su sanya labarin ya gundure su, za su kuma sanya su kasa fahimtar hakikanin sakon da yake so ya isar. Ba an ce kada a rika aro kalmomi daga wadansu harsuna ba, a’a, a rika aron kalmomin da harshen Hausa ya hadiye su, ko kuma idan an aro wadanda harshen Hausa bai hadiye su ba, sai a sanya su a baka, ko kuma a yi karin bayani a kan su.
Wadansu abubuwa da za su taimaka wa marubuci wajen rubuta kirkirarren labari sun hada da:
. Waiwaye (Flash Back ko Foreshadowing): Ba a so marubuci ya saki labarinsa sakakaka, wannan zai sanya masu karatu su rika hasashen abin da zai faru a gaba, dalilin haka ne ake so marubuci ya rika wasa da hankalin masu karatu har su kasa hasashen abin da zai faru a gaba, inda za su rika bin labarin sau-da-kafa. Waiwaye zai samu ginshikin kafuwa ne, ta hanyar gina labari bisa sigar yin gaba da kuma dawowa baya, wannan kuwa zai yiwu ne, idan marubucin ya rika boye wadansu batutuwa dangane da labarin.
. doki (Suspence): Ana so marubuci ya gina labarin da zai sa masu karatu su rika doki da alla-alla wajen ci gaba da karanta labarinsa don jin abin da zai faru. Ma’ana, ana so ya sanya labarin a turbar da masu karatu za su ji ba sa son motsawa ko da nan-da-can ne, har sai sun kammala karanta littafin. Hakan kuwa zai samu ne, idan marubuci ya samu jigon labarin (theme) mai gamsarwa, idan marubuci ya samu salo (style) mai dadi da daukar hankali, haka idan zai iya yin waiwaye (flash back) a lokacin da ake bukatar a yi waiwayen, da sauran abubuwa masu jan hankalin masu karatu.
Gina Labari (Story Plot): Wannan ya kunshi gina labari a takaice da fadada labarin da fitar da labari bisa sigar babi zuwa babi da salon labari da jigon labari da kuma waiwaye da sanya doki da sauran batutuwa. Don haka ne ake so marubuci ya yi taka tsan-tsan wajen fitar da jadawali da kuma manhajar labarinsa bisa zubi-da-tsari mai kayatarwa da kuma kyawu. Rashin amfani da abubuwan da na ambata a sama kuwa zai iya bata ginin labarin har ya rusa shi gaba daya.
Misali, marubuci ya ce zai yi rubutu a kan bishiyar da babu ita, to za ka rika tambayar kanka yaya launin bishiyar zai kasance? Ganyayyakinta fa? Dogayen reshe take da shi ko a’a? Yaya ’ya’yanta za su kasance? Suna da zaki ko daci? Bishiyar tana magani? Ko illa take da shi? Yaya girmanta zai kasance? Wadanne kalmomi zai yi amfani da su bayaninta? Wane salo zai yi amfani da shi? da sauransu.
Kada marubuci ya rika kwaikwayon wadansu marubuta, ya samar da nasa salon. Ya zabi yadda labarinsa zai kasance, mai yawa ne ko kuma kadan. Don samun saukin aiki ma zai iya rubuta taba ka lashe ko dandano a kan labarin, wanda zai taimaka a lokacin da yake rubuta labarinsa.
Ana so marubuci ya mayar da hankalinsa wajen duba kura-kurai yayin rubuta kalmomi, idan bai yi hakan ba, sai ya isar da sakon da ba shi yake son isarwa ba. Daga nan ya maimaita karanta littafin a hankali, don gano wadansu kura-kurai.
Wadansu dabarun da za su taimaka wajen rubuta labarin kirkira sun hada da:
. Marubuci ya tabbata ya tsara labarinsa, sannan ya samar da wata matsala da za ta rika jan hankalin mai karatu har zuwa lokacin da zai samar da maslaha dangane da ita. Misali, labari a kan garkuwa da mutane, ko matsalar fashi da makami ko ta kisan kai, sai ya rika jan zaren labarin har ya samar da maslaha dangane da matsalar da ta taso.
. Murubuci ya tabbata bai kauce bin ka’ida a kan labarin da yake bayarwa ba, misali yana ba da labari a kan kisan kai, sai ya yi wani abu da ya saba shari’a ko ka’ida a zahiri, kada ya ce don yana rubuta labarin kirkira, to zai rubuta abin da ya ga dama, idan masu karatu suka lura da haka za su daina karanta littafinsa.
. Lokacin da yake rubata labarin ya tabbata babu wani abu da yake damunsa, sannan ya rika tunanin dacewa ko rashin dacewar duk wata jimlar da zai yi amfani da ita a labarinsa.
. Ya daina daukar lokaci wajen rubuta labari, ma’ana idan ya yi rubutu yau, ba zai sake yi ba, sai bayan wata uku ko hudu, hakan zai sanya ya rasa wadansu abubuwa a cikin labarinsa. Wani lokaci kuma zai iya manta wadansu abubuwa dangane da labarin har ya koma kame-kame.
. Idan har ya fara rubuta kirkirarren labari, to ya tabbata yana rubutu kowace rana ko mako, domin hakan zai taimaka wajen kulla zarurrukan labarinsa.
. Ya tabbata yana da sha’awa a kan labarin da yake rubutawa, hakan zai sanya labarin ya kayatar.
. Ya dauki rubutu a matsayin sha’awa ba wai don neman kudi ba, idan ya yi hakan lokacin da zai samu kudi ta hanyar rubutu ba zai ma sani ba.
. Ya rika bincike sosai kafin ya fara rubuta labari a kan duk jigon da yake so bayar da labari a kai.
. Ya rika amfani da sunayen wadanda suka shafi al’ummar da yake ba da labarin don su, yin hakan zai sa su gane da su ake yi, ba wai da wadansu a wata duniya ba. Zai fi kyau ya dauki wata matsala da ke damun al’umma sai ya yi labarinsa a kan ta, hakan zai fi yi musu tasiri.
. Kada ya rika yawan maimaita kalmomi hakan zai sanya labarin ya gunduri masu karatu, za su rika jin kamar yana ci da karfi ne wajen rubuta labarinsa.
. Zai fi kyau da kuma daukar hankali ya rika rubuta labarinsa daga babi zuwa babi, sannan ya guji yin dogayen sakin layuka, hakan na gajiyar da masu karatu.
. Kada ya samar da matsalar da za ta dauki lokaci ba tare da ya samar da maslaha a kan ta ba. Kada ya tara kalmomi barkatai.
. Ya kamata marubuci ya ba da damar da masu karatu za su rika yawo a cikin labarinsa, sannan ya rika sanya musu tambayoyi, sannan ya rika ba da amsa, hakan zai sa ya rike su har karshen labarinsa.
. Ya rika amfani da sunayen da ba za a sha wahala wajen tuna su ba, zai iya amfani da sunaye masu dadi da kuma kama hankali.
. Kada ya dauki jigogi masu yawa a cikin labarinsa, ma’ana ya dauki jigon kiwon lafiya da siyasa da soyayya da illar son kudi kuma auren dole, hakan zai rikitar da masu karatu, su rasa bangare za su fi mayar da hankali. Idan ya dauki jigogi uku ko biyu, zai samu damar yawo daga wannan jigo zuwa wancan, ba tare da ya gunduri masu karatu ba.
. Ya tabbata ya zabi kalmomin da za su dace da kowane irin jigo ya dauka. Kada ya yi gaggawa wajen rubuta labari, domin hakan zai sanya a samu kura-kurai masu yawa a labarinsa.
A karshe ina fata wannan bayani zai gamsar da duk mai bukatarsa.