✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Da’awa da sulhunta jama’a ne manyan ayyukan Jama’atu – Salisu Liman Iya

Sakataren kungiyar Jama’atu Nasril Islam ta kasa reshen Masarautar Suleja da ta kunshi kananan hukumomin Suleja da Gurara da Tafa a Jihar Neja Alhaji Salisu…

Sakataren kungiyar Jama’atu Nasril Islam ta kasa reshen Masarautar Suleja da ta kunshi kananan hukumomin Suleja da Gurara da Tafa a Jihar Neja Alhaji Salisu Yakubu Liman Iya ya ce muhimman ayyukan da kungiyar take gudanarwa a masarautar su ne aikin da’awa da aka kafa ta dominta da kuma na sulhunta jama’a.

Alhaji Salisu Liman Iya ya bayyana haka ne lokacin da suke tattaunawa da wakilinmu a garin Suleja a ranar Asabar da ta gabata, inda ya ce kungiyar tana gudanar da da’awa na kira a bainar jama’a da da’awa ta hanyar shirya laccoci da kuma da’awa ta hanyar aika malamai suna zagaya masallatai suna gudanar da wa’azi.

Ya ce a bangaren da’awa a kowace shekara sukan samu wadanda suka Musulunta akalla mutum 20 zuwa 30.

Ya ce, jama’ar Musulmi suna bayar da gudunmawa ga kungiyar gwargwadon iko, amma babban wanda ya fi tallafa mata shi ne Mai martaba Sarkin Suleja Alhaji Muhammad Awwal Ibrahim, inda Sakataren kungiyar ya ce, “Shi ne kashin bayan duk harkokin tafiyar kungiyar kama daga kula da wadanda suka musulunta da sauransu. Ya ce ma kada ya ji kungiyar ta masarautar ta fita waje neman tallafi, sai idan abin ya gagare shi, zai bayar da umarni a fita neman. Kuma alhamdulillahi, tunda ya shigo wannan gida Sarki bai taba kasawa ba, duk lokacin da muka nemi taimako yana yi mana.”  

Malam Salisu Liman Iya ya ce, a bangaren sulhunta jama’a kungiyar tana shiga tsakani domin sulhunta ma’aurata da makwabta da ’yan kamar yadda addinin Musulunci ya tanada. Ya ce, manufar yin sulhuntawar ita ce domin a tabbatar kyakkyawar dangantaka a tsakanin Musulmi, ta yadda a wasu lokuta koda an je kotu sukan nemi alkalai su ba kungiyar dama ta sulhunta masu takaddamar, kuma alkalan na ba su dama. Ya ce idan batun ya yi tsauri sukan shigo da limamai cikin batun domin su sasanta, kuma ana samun nasara. 

Sakataren ya ce akalla a kowane wata sukan sulhunta rikicin da suke tasowa a tsakanin masallatai ko tsakanin ma’aurata biyar zuwa 10 a kowane wata.

Ya ce matsalolin da suka fi fuskanta su ne kasancewar ba a ba malaman alawus ko albashi a wasu lokuta sukan fuskanci karancin gudanar da ayyukan da kungiyar take shiryawa.

Sai ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su rika amfani da dukiyarsu wajen taimaka wa addini. Ya ce masu hannu da shuni kuma masu zuciya su rika hada hannu da kungiyar da sauran kungiyoyin addinin Musulunci domin daukaka addinin.

Ya yaba kan kyakkyawar dangantakar da ake samu a tsakanin kungiyoyin addinin Musulunci da suke masarautar musamman yadda Mai martaba Sarkin Zazzau na Suleja yake rungumar dukan kungiyoyin Musulunci a masarautar.